ZARGIN CUWA-CUWA: Fashola ya maida wa Dino Melaye raddi

0

Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya yi Allah wadai da Sanata Dino Melaye, dangane da abin da ya kira ‘kage da kazafin da ya yi na wuru-wuru a ma’aikatar sa.

Dino Melaye dai ya rubuta takardar korafi ne a matsayin neman kudiri a majalisa inda ya zargi yadda aka yi asarkala da kudi kimanin Dalar Amurka milyan 35 a ma’aikatar.

Bayan wannan kuma, sanatan ya kara da cewa an kuma yi wani yunkurin arcewa da wasu zunzurutun dala milyan 350 a ma’aikatar ta Fashola.

Sai dai kuma da ya ke maida wa Melaye martani, a wata wasika da ya sa wa hannu da kan sa, ministan ya ce ma’aikatar sa ko wasu ma’aikata a ma’aikatar sa ba su aikata wata zamba ba, kuma za su hada kai da kwamitin duk da zai zo ya yi bincike.

Fashola ya kara da cewa a 2013 dai ba shi ne minista ba, kuma a waccan shekarar ne Melaye ya ce an ci kudin. Ya kuma ce nauyin kula da wani bashi da wata ma’aikata ta ciwo, musamman ya Euro, ya dogara ne a kan Ofishin Kula da Harkokin Bashi, ba hakkin ma’aikatar sa ba ne.

Fashola ya ce kawai dai akwai wata mummunar manufa boye a zuciyar Dino Melaye, shi ya sa ya ke kirkiro karairayi da zarge-zarge na sharri a kan ma’aikatar sa.

“In ban da wata boyayyar manufa, ai wannan dalili kadai ma ya isa mutum ya gane cewa maganar ya kai wannan batun a majalisa ma ba ta taso ba, domin kuwa ga hujjojin mu nan kowa ya sani.” Cewar Fashola.

Share.

game da Author