Zanga-zangar direbobi ta tsaida harkoki a Abuja

0

Harkoki sun tsaya cak a yawancin wurare a Abuja, yayin da direbobi masu zanga-zanga su ka tare dukkan hanyoyi da su ka nufi Kasuwar Wuse, wadda ita ce babbar Kasuwa a Abuja.

Zanza-zangar ta biyo bayan harbe wani direban taksi da wani soja ya yi, wanda ke cikin tawagar kwamitin Task Force, wanda ya kunshi sojoji, ‘yan sanda, jami’an VIO, dakarun tsaro ‘yan Civil Defence.

PREMIUM TIMES ta garzaya bakin Kasuwar Wuse, sai dai tun kafin isar ta, ta iske jami’an tsaro sun yi sauri sun dauke wanda su ka harba sun gudu sa shi.

Yayin da wasu ke cewa a nan take direban da aka harba din ya mutu, wani kuma ya shaida cewa bai mutu ba, amma garzayawa aka yi da shi zuwa asibiti. Hatta babban titin nan Sani Abacha Way, wanda ya tashi daga babban shatale-talen Life Camp zuwa Babban Masallacin Juma’a na Auja, shi ma an hana motoci wucewa, yayin da masu zanga-zangar su ka cunna wuta a karkashin gadar Kasuwar Wuse.

A gaban wakilin PREMIUM TIMES hasalallu su ka cunna wa tayoyi wuta a karkashin gadar, ta yadda babu hanyar da motoci za su wuce.

Wata motar kashe gobara dauke da jami’an hukumar kashe gabara da ta garzaya wurin domin kashe wuta, an hana ta gudanar da aiki, domin a gaban wakilin mu mafusatan matasa su ka bi motar a guje su na jifa.

Ita kan ta kasuwar ta Wuse, ta kasance a rufe, yayin da jami’an tsaro su ka rufe kofar shiga, sai dai a fita kawai.

Wani direba da ya shaida wa wakilinmu cewa a gaban sa abin ya faru, ya ce “wani soja ce ya dirka wa direban taxi dindiga, inda ko da da su ka ga ya fadi, sai su ka yi sauri suka dauke shi su ka jefa motar su, suka arce, don kada mafusata su yi musu rubdugu.”

Shi kuwa wani direba mai suna Emmanuel, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa “wadannan jami’an tsaron fa shaidanu ne kawai, kuma ‘yan cuwa-cuwa. A kullum su na kama mu su na karbar kudade daga hannun mu, ba tare da su na mika kudin ga gwamnati ba, tunda ba rasidi su ke ba mu ba.”

Shi ma wani direba mai suna Danladi, ya shaida wa wakilin mu cewa an sha kama shi kamar sau shida. “A kowane kamu da ake yi min, ko dai sun raba ni da naira dubu shida, dubu bakwai, kai har ma dubu 15,000.”

“Na rantse maka da Allah ni fasto ne, don haka ba zan yi maka karya ba. Duk kamu da su ke yi min idan na biya tara, sai dai na karbi mota ta kawai, amma ba su ba ni rasidi. Ka ga hakan na nuna cewa su ke raba kudin a tsakanin su kenan.”

Shi ma Malam Garba, cewa ya yi hatta masu KEKE NAPEP idan aka kama su, ana karbe musu naira dubu bakwai zuwa dubu goma.

“Joshua da Ibrahim sun zo gaban wakilin PREMIUM TIMES su na kartsa kuwwa: “Ba ma son ‘yan task force, sai dai a yi duk wadda za a yi.”

PREMIUM TIMES ta lura da cewa akwai alamomin barkewar rudani, yayin da ta ji wasu matasa masu jajayen idanu na barazanar cewa, “mu je mu cunna wuta a ofishin task force da ke Wuye.”

Share.

game da Author