Shahararren matashi dan wasan fina-finan Hausa, Abdul Shareef ya sanar wa PREMIUM TIMES HAUSA, cewa soyayyar da ya ke yi wa fina-finai ne ya sa ya shiga harkar gadan gadan.
Bana dai shekarun Abdul 5 kenan yana fitowa a finafinan Kannywood kamar yadda ya sanar wa wakilin mu da yayyi hira da shi.
Wata mai yin sharhin, Hassana Dalhat, ta ce ” Ganin cewa dan uwan Abdul wato Umar ya shahara wajen rera wakoki dayawa daga cikin mu mun dauka shi kansa Abdul zai bi sahun Umar ne, sai gashi ya zama jarumin gaske a harkar fim.”
Abdul ya ce tun farko shi baiyi sha’awar yin waka ba. ” Dama can ni fim nake sha’awa kuma burina ya cika yanzu domin ana fafatawa da ni. Ko da yake kafin na fara fitowa a ganni a fim, na dade ina rubuta labari, kuma ni kai na furodusa ne.”
Abdul ya ce tun da ya fara fim ya mai da hankalinsa wajen ganin ya dada kwarewa da kuma ganin cewa yayi fice a abin da ya sa a gaba.
” Ni bani da wani abu da na sa a gaba yanzu in da harkar fim ba. Kuma zan ci gaba da haka babu ranar dakatawa InshaAllah.”
Ya kara da cewa Shi mutum ne da yake iya hawa kowace irin kujera aka bashi ya hau a fim kuma burin sa shine ya zama dan wasan da za a ji shia duk duniya.
” Ba Kannywood ba kawai, ni burina shine a ce an jini duk duniya. ”
Abdul yana da aure da ‘ya’ya uku sannan fitaccen masanin addinin musulunci ne.
” Idan bana fim toh, ina tunanin fim ne.”
Discussion about this post