Wani malami a jami’ar Legas dake koyarwa a sashen koyar da aikin likita, Ifedayo Odeniyi, yace cutar siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.
” Shi Insulin ya na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki. ”
Ya kuma kara da cewa rashin aikin sa ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da cutar siga.
Bayan haka kuma ya yi kira ga mutane da su yi watsi da camfin da ake yi wai shan zaki ne ke kawo cutar siga.
Ya ce hakan ba gaskiya bane.
” Likita ya ce saboda irin wannan camfe-camfe ne ya sa mutane ke hana kansu cin abinda ya kamata don samun kuzarin da suke bukata a jikin su.”
Ya ce tabas yana da mahimmanci idan mai dauke da cutar siga na kiyaye sharuddan da ya shafi irin abincin da ya kamata ya ci, amma haka ba yana nufin kada mutum ya hana kan sa cin abincin da ke da sinadarin ‘Carbonhydrates’ saboda samun kuzari a jikin su.
Likita Odeniyi ya ce cutar siga yakasu kashi kashi; Akwai wanda shi Insulin baya aiki kwata kwata a jikin mutum wanda ake kira da ‘Type 1diabetes’ sannan akwai wanda shi insulin din yana aiki amma ba yadda ya kamata ba wanda ake kira ‘Type 2 diabetes’ shine mafi yawan ‘yan Najeriya ke fama da shi.
Ya ce alamomin cutar su hada da yawan jin yunwa, yawan yin fitsari da sauransu.
Bayan haka Oladimeji Agbolade ma’aikacin kamfanin sarrafa magunguna dake kasar Faransa ‘Sanofi’ya ce kula da masu dauke da cutar siga na da matukar wuya ganin yadda magungunan cutar ke da tsada gaske.