Wakilan jam’iyyu daban-daban sun raba abinci, abinsha har ma da raba kyautar kudade a rumfunan zabe, da nufin a ja hankalin masu kada kudi’a su zabi na su ‘yan takara. PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka.
Wakilan jaridar nan da abokan aikin-hadin-guiwar sun a kungiyar CCD, sun gane wa idanun su yadda ejan-ejan na jam’iyyar APGA mai mulkin jihar ta Anambra da kuwa ejan na PDP suna raba kudade da abinci a wurin zabe.
A wasu wuraren, masu kada kuri’a sun rika damka katin zaben su ga wadanda ke raba musu kudi.
A Dandalin Illo Abito da ke Nsugbe, inda dan takarar gwamna daga APC, Tony Nwoye ya jefa kuri’ar sa, an rika ganin yadda ake raba wa masu kada kuri’a abinci, wasu ma har da rububi.
Can a Mazabar Okija Ward 2, PU009, da ke cikin firamare ta Umuohi kuwa, wakilan mu sun ga ejan da ake zargi na PDP, APC da APGA ne sun a raba dumbujen kudi. An ga lokacin da ake damka wa masu jefa kuri’a naira 500 kowane.
A mazabun Umedim 1 cikin Otolo, Karamar Hukumar Nnewi ta Arewa, an ga dafifin jama’a sun hau layuka inda ejan na APC da na APGA su na raba wa jama’ar su nairori.
Wakilan PREMIUM TIMES sun kara ganin yadda aka raba kudi a mazabu daban-daban, ciki har da Mazabar CPS Odekpe Ward 5 da ke cikin karamar hukumar Ogbaru, inda ejan na PDP ya rika raba naira 2000.
Sannan kuma an ga ejan na APGA na raba wa masu jefa kuri’a Maltina mai sanyi tare da Gala a rumfar zabe ta cikin firamaren Abatete.