Gwamna mai ci na jihar Anambra, Willie Obiano, ya sha caccaka yau a wurin masu rajin kare hakki daga kungiyoyin sa-ido a zaben jigar Anambra.
Sun ce jawabin da ya yi wa jama’a a wurin zabe, kamfe ne kai tsaye ba wani abu ba, domin INEC dai ta haramta a yi kamfe awa 24 kafin a fara jefa kuri’a.
Gwamnan dai ya jefa kuri’a karfe 10 na safe a Firamare ta Eri, Rumfar Zabe mai lamba 004, Otoucha 1, a Karamar Hukumar Anambra ta Gabas, daga nan kuma sai ya balle yi wa magoya bayan sa jawabi.
Abiola Akiyode na kungiyar Transition Monitoring Group, kungiyar da ke sa ido kan yadda ake gudanar da abe, ya yi tir da dabi’ar gwamnan.
“Abin takaicin ma shi ne yadda gwamnan ya je rumfar zabe da makirfo ya na yi wa jama’a jawabi. Ni ina ganin wannan kamfe ya yi ba wani abu ba. Tun da na ke sa-ido kan zabuka, ni dai ban taba ganin inda gwamna ya je wuri zabe ya na yi wa magoya bayan sa jawabi ba. Kuma abin mamaki har da yin amfani da makirfo.