Gwamnonin Najeriya sun ce za su iya biyan ma’aikatan Jihohin su ne kawai idan Buhari ya sa hannu suka samu sauran kudaden ‘Paris Club’ da ya rage.
Gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya shaida wa manema labarai haka bayan ganawa da gwamnonin suka yi da shugaban Kasa yau a Aso Rock.
Okorocha ya ce lallai suma suna so mutane su ji dadin bukin Kirismeti sai dai rashin kudi da suke fama dashi ne zai iya kawo cikas akai. Amma idan har Buhari ya sakar musu kudin ‘Paris Club’ kowa fa zai sha jan miya a Kirismeti.
” Maganan albashin ma’aikata shine Kan gaba a abubuwan da muka tattauna da Buhari, sannan ya ce zai yi kokarin ganin Jihohin sun sami wadannan kudade da suke bukata.”
Shima gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce wasu gwamnonin ba za su iya biyan ma’aikatan su ba ko an basu kudin ‘Paris Club’ sai dai rabin goro yafi babu, zasu samu ko da rabi ne.
” Mu dai a jihar Kaduna ba mu da matsalar albashi, ko da an bamu kudin ‘Paris Club’ sai dai mu karkatar dasu wajen yin wasu aiyukan. Haka ma jihar Kano bata da wannan matsala.” Inji El-Rufai.
Discussion about this post