Kungiyar likitoci mata na Najeriya SOGON ta ce za ta kashe Naira miliyan 4 don fida da kula da matan dake fama da cutuka a wasu kauyuka a jihar Sokoto.
Shugaban asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Dan Fodiyo Yakubu Ahmed yace likitocin za su tallafa wa mata 200 kuma kyauta.
Cutukan da likitocin za su duba sun hada da cutar yoyon fitsari, cutar daji da sauransu.
Discussion about this post