Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce gwamnati za ta samar wa mutane na’urar gwajin cutar kanjamau wanda ba sai sun je asibiti ba. Zasu yi gwajin dakan su ne a dakunan su.
Adewole ya sanar da haka ne da ya ke karbar bayanan rahoto kan ingancin na’uran gwajin da ma’aikatan lafiya tayi.
Isaac Adewole ya ce bincike ya nuna cewa miliyan 5.9 na mutanen Najeriya na dauke da cutar kanjamau sannan a duniya gaba daya mutane miliyan 14 na dauke da cutar amma basu sani ba.
Ya ce matsaloli kamar rashin sani, tsoro, kunya da makamantan su na sa mutane na kin neman sanin matsayin da lafiyar su ke ciki.
Ya ce saboda kawar da irin haka ne ya sa ma’aikatar ta shigo da wannan na’ura domin rabawa mutane.
“Hakan zai samar wa mutane sirrin da suke bukata sannan zai sa mutum yasan inda ya sa gaba.