Ma’aikatar tsaro ta saki kudade don biyan alawus din dakarun Najeriya dake fafatawa da Boko Haram.
Darektan yada labarai janar Sani Usman ne ya sanar da haka inda ya ce babban hafsan dakarun Najeriya Tukur Buratai ya sa hannu akan haka ranar litini.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda sojoji ke kuka Kan rashin biyan su alawus din su na watanni biyu.
Daga karshe Buratai ya jinjinawa dakarun Najeriya na hakuri da suka yi da Nina kishin Kasa da suke yi.
Ya kuma jaddada musu cewa za ana biyan su alawus din su akan lokaci.