Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Jimoh Moshood yace sun kashe mutane biyu cikin wadanda ake nema ruwa a jallo game da kisan shugaban ‘yan banga Haruna Maikaji a kauyen Sabon Gayan, dake titin Kaduna zuwa Abuja.
Moshood ya ce sun harbe mutane biyu bayan arangama da suka yi a kauyen.
Moshood ya ce sun yi haka ne bisa ga umurnin da shugaban rundunar ‘yan sanda Idris Ibrahim ya basu da su tabbata sun kama duk mutanen da suka aikata wannan kisan.
Idan ba a manta ba ranar 12 ga watan Nuwamba PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa matasan kauyen Sabon Gayan sun hana wucewa a babban titin Abuja/Kaduna sanadiyyar kisan da wasu masu garkuwa da mutane suka yi wa shugaban kungiyar ‘yan bangan su Haruna Maigona yayin da yake aiki a gonar sa ranar Lahadin da ya gabata.
Moshood ya ce ‘yan sanda na farautar sauran wadanda suka aikata wannan kisa.