‘Yan sanda sun kama barayin yara masu karbar katin waya kafin su sake su a Kano

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano Magaji Majia ya ce sun kama wasu mutane uku dake satan yara a jihar.

Magaji ya ce sun kama su ne tare da yara 7 da suka sace.

” Barayin yaran sukan bukaci a iyayen yaran da suka sace ne da su aiko musu da katin waya na iya kudin da suke bukata kafin su saki yaran. Iyae kuwa sukan bi umarnin masu garkuwan su tura musu katin waya na iya abin da suke bukata. Sannan idan suka sace yaran sukan kai su unguwan da ba kusa da inda suke zaune bane.”

Wani cikin barayin mai suna Kalifa Usman ya ce sun yi hakan ne domin kada yaran su wahala sannan kuma da rashin wurin ajiyan su.

Majia yace sun kwato yara 7 daga wurin barayin, wayan tarho daya, layukan wayan uku sannan da katin lodi da dama.

Share.

game da Author