Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa ‘yan bautar kasa ne suka haddasa rashin fara jefa kuri’a da wuri a wasu wuraren kada kuri’a, a zaben Anambra.
Mai magana da yawun hukumar, Solomon Soyebi, ya ce yawancin rumfunan zabe ba su bude da wuri ba, saboda masu bautar kasa da aka dauka aiki, ba su bi dare zuwa wuraren da aka tura su gudanar da aikin zabe ba.
Soyebi, wanda shi ne babban jami’in ilmantawa da yada Labarai na INEC, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an samu ‘yar matsala ce daga masu bautar kasa, musammam wadanda aka dauko daga wasu jihohi makwabta.
A Awka-ta-Kudu, Soyebi ya ce sai da ta kai INEC ta tura ‘yan bautar kasa har 180 zuwa Nnewi ta Arewa da ta Kudu da misalin karfe 8:30 na safe. To wannan a ta bakin sa, ya dan tawo lattin farawa da wuri.
Sai dai ya bada tabbacin cewa kalubalen da aka samu, kamar na rashin tantance wasu da na’urar Card Reader ba ta yi ba, ba zai shafi zaben ba.