Wasu mata dauke da bam sun yi sanadiyar mutuwar wasu mutane 4, wasu 6 kuma sun sami raunuka, bayan sun tada bam din dake daure a jikin su.
Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES wani shugaba a kungiyar sa kai ‘Civilian-JTF’, Danbatta Bello ya ce tun daga karfe 8:20 zuwa 9:51 na safe ne aka fara jin tashin bama-bamai a yankin.
Matan wanda su hudu ne sun ta da bama-baman ne a kusa da katangar jami’ar Maiduguri.
“Daya ta yi saurin tada na ta bam din tun kafin ta kai ga jikin katangar amma sauran uku sai da suka kai sannan suka tada bam. Hakan ya sa wasu manoma sun sami raunuka dalilin haka.