‘Yan bindiga sun kasahe mutane 11 a Filato

0

Wasu ‘yan bindiga sun harbe mutane 11 har lahira a hanyar su na dawowa daga cin kasuwar kauyen Makera dake karamar hukumar Riyom, jihar Filato.

Jami’in hurda da jama’a na rundunar ‘Yan sandan jihar Filato Terna Tyopev, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar harin.

Ya ce ‘yan sanda sun fantsama neman wadanda suka aikata wannan abu.

Har yanzu babu wata kungiya da ta fito ta ce ita ta aikata wannan mummunar aiki.

Share.

game da Author