YAJIN AIKI: Saka baki da dattawa suka yi ne ya sa muka janye yajin aiki – Marafa

0

Kungiyar kwadago reshen jihar Zamfara ta janye yajin aikin da ta shiga watanni biyu da suka wuce sanadiyyar rashin biyan ma’aikata albashi, alawus, fansho da sauran su da gwamantin jihar ba ta yi ba.

Shugaban kungiyar Bashir Mafara ya sanar da haka inda yace sakamakon tsoma baki da wasu dattawan jihar suka yi ne ya sa suka janye yajin aikin.

Daga karshe kungiyar ma’aikatan ta jinjina wa dattawan jihar saboda baki da suka sa aka samu maslaha.

Sannan sun yabi gwamnatin jihar kan amincewa da ta yi na biyan ma’aikatan.

Share.

game da Author