Yadda masu hura usur suka taimaka min a EFCC – Ribadu

0

Shiga da tsarin hura usur ga wadanda suka wawuri dukiyar al’umma ya kawo nasarori wajen saukaka gurfanar da wasu manyan harkalla da satar kudi da aka yi tsakanin 2003 da 2007, haka tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya bayyana.

Tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadau, ya hori ‘yan Najeriya da su karbi tsarin hura usur, wato tona asiri ko fallasa manyan barayin gwamnati a matsayin babbar hanya ta magance cin hanci da rashawa da suka yi wa kasar nan kaka-gida, kuma abin ke kawo cikas wajen ci gaban kasa.

“Mafi yawan shari’un da muka yi nasara kan wadanda suka wawuri dukiyar jama’a, duk an tona asirin su ne ta hanyar hura usur.” Haka Ribadu ya bayyana a wani taro da aka gudanar a kan rashawa da cin hanci a Abuja.

Cibiyar Kafafen Yada Labarai da Sadarwa ta AFRICMIL ta shirya taron da hadin guiwar Kwamitin Majalisar Tarayya a kan zambar kudade, SERAP da kuma cibiyar Wole Soyinka ta Binciken Kwaraf na Aikin Jarida.

Ribadu dai an cire shi daga shugabancin EFCC ne a zamanin mulkin Umaru Yar’Adua cikin 20017. Ya ce a lokacin sa EFCC ta bai wa masu tinon silili muhimmanci sosai, domin a dakile cin hanci a ma’aikatu. Sai ya jinjina wa gwamnatin Buhari da ta rungumi shirin da muhimmanci.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shigo da tsarin hura usur, tare da yin alkawarin bayar da kashi 5 bisa 100 na kudaden da da aka kwato daga hannun wanda ya wawuri kudin.

Gwamnatin Tarayya kuma ta ce ta biya ladar hura usur har naira miliyan 400 a farkon watanni shida na 2017.
Wannan tsari dai ya taimaka wa gwamnati ta karbo makudan kudade, wadanda ba don haka ba, da gano su zai yi matukar wahala.

Share.

game da Author