Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya kara jefa kafar sa cikin wata sabuwar tsomomuwa. Sunan sa ya sake bayyana a ranar Lahadin nan a cikin wani jerin sunayen mashahuran ‘yan siyasa na duniya wadanda aka samu dumu-dumu wajen boye kadarori, kin biyan haraji da kuma karkatar da kudaden talakawa.
An samu sunan Saraki ne cikin wata kashe-mu-raba da ta gudana da kamfanin Shell. Wannan harkalla da aka fallasa za ta iya haifar masa da wata sabuwar tuhuma, watanni 18 bayan wani bincike ya same shi da hannu dumu-dumu a cikin harkallar mallakar kamfanoni uku a asirce, wadanda ya ke amfani da su ya na boye kudade a kasashen waje.
Wannan sabuwar fallasa ta zo ne a daidai lokacin da ya ke ta gaganiyar wanke kan sa daga zargin yin rantsuwar kaffara wajen bayyana kadarori, ta hanyar yin kwangen ainihin yawan kadarorin da ya mallaka. A yanzu dai tuhumar da ake yi masa kan kwangen adadin kadarori na a gaban Kotun Daukaka Kara.
A wani bincike da PREMIUM TIMES ta yi, tare da hadin kan kungiyar ‘Yan Jarida Masu Biciken Kwakwaf na Duniya, sun gano cewa Saraki ne shugaban hukumar gudanarwar wani kamfani na kasar waje tun daga lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara, har zuwa lokacin da ya ke a Majalisar Tarayya.
A cikin 2001, Saraki ya kafa wani kamfani mai suna Tenia Limited can a Tsibirin Cayman, wani tudun-mun-tsirar harkalla da badakala a yankin Caribbean.
Ya ci gaba da rike shugabancin kamfanin a matsayin darakta, wanda kuma shi kadai ne ke da hannun jari a cikin sa.
Ba a dai san irin harkalla da daka-dakar harkokin da Saraki ya rika yi da sunan, haka kuma ba san adadin kadarorin da ya kimshe a kamfanin ba.
Sai dai kuma inda matsalar ta ke, shi ne Saraki bai lissafa Tinea Limited a cikin jerin kadarorin da ya mallaka ba, a lokacin da aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kwara cikin 2003. Hakan ya na nufin cewa kuru-kuru Saraki ya karya dokar CCT. Haka nan Saraki bai lissafa da sunan kamfanin ba a 2007 lokacin da aka sake zaben sa gwamna da kuma 2011, da kuma lokacin da aka zabe shi Sanata.
Wannan sabuwar fallasa da aka yi wa Saraki da sauran dimbin wasu shugabanni na duniya, ya fito ne daga tonon-sililin-zare da wata jaridar kasar Jamus mai suna Suddeutsche Zeitung tare da hadin guiwa da ICIJ suka yi, daga cikin wani bayanin sirri da ya fito daga wata kafar soshiyal midiya mai tara bayanan sirri, wato Appleby and Trust.
Ma’adinar bayanan sirrin mai lamba 1.4 terabyte, a yanzu an fi sanin ta da sabon sunan da aka rada mata, wato PARADISE PAPERS. Ta na kunshe ne da bayanan sirri har milyan 13.4, kuma ita ce ma’adanar bayanan sirri mafi girma a tarihin fallasa harkalla a duniya.
Sai da ka shafe sama da shekara daya, wasu mashahuran ‘yan jarida har 380 daga kafafen yada labarai 96 da ake da su a kasashe 67, su ka fantsama cikin Paradise Papers, ma’adinar bayanan sirri na kusan shekaru 70, daga 1950 zuwa 2016. PREMIUM TIMES ita kadai ce jaridar da ke cikin wannan bincke na musamman.
An binciko sunayen manyan ‘yan siyasa na duniya da shugabanni 120 daga kasashe kusan 50 da kuma dimbin hamshakan ‘yan kasuwa daga kasashe na duniya, duk an same su da mallakar kamfanoni a kasashen waje inda su ke boye wata harkalla da hauma-haumar da ba su hukuma da gwamnatocin kasashen su su sani.
Paradise-Papers-Sarkin-Tonon-Silili
Abin da aka fallasa daga Paradise Papers ya zo watanni 18 bayan da Panama Papers su ka gigita duniya da rahoton yadda aka rika amfani da kamfanin hakar danyen man fetur na Shell a duniya, ana harkalla.
An kuma hakkake cewa akwai sama dalar Amurka triliyan 32 a asusunn ajiyar irin wadannan kudaden lukudi, wadanda gwamnatocin kasashen su ba su amfana da su ta hanyar su rika biyan haraji ana karuwa da su.
Yayin da Tenia Limited ba a cikin kamfanonin Saraki wadanda Panama Papers ta fallasa, Paradise Papers ce ta fallashi a ranar Lahadi da ta gabata.
Wani lauyan Saraki da ke Lodon, Andrew Stephenson, ya tabbatar da cewa tabbas Tenia Limited mallakar Saraki ne. Sai dai kuma ya ce kamfanin ba ya gudanar da harkokin sa a cikin sirri, kuma bai karya kowace irin doka ba.
Yayin da PREMIUM TIMES ta tambayi dalilin da ya sa Saraki bai taba bayyana shi a cikin kadarorin sa ba, sai Stephenson yace a bashi dan lokaci kafin ya tuntubi Saraki, sannan zai bada amsa.
Ya dai nanata cewa Tenia Limited ba ya da wani kwakkwaran jari kuma ba ya ma gudanar da kowace irin hulda ta kasuwanci.
“Tun daga ranar da aka kafa kamfanin har zuwa yau din nan, bai taba gudanar da harkokin kasuwanci ko da guda da yaba.” Inji lauyan na Saraki.