Wani soja ya bindige Ogan sa ‘Captain Mani’ har lahira

0

Wani Soja mai suna Silas Ninyo ya bindige Ogan sa mai mukamin captain har lahira sannan ya dirka ma kansa harsashi shima.

Captain Mani ya gamu da ajalinsa ne bayan wani sako da ya samu a daidai ya na sintiri a wasu yankunan Madagali, dake jihar Adamawa, cewa ga wani soja nan na dukan mutane babu gaira babu dalili.

Daga nan ne fa yaja ayarinsa zuwa wajen, nan da nan kuwa suka yi iya kokarin su wajen hana Silas ci gaba da abin da yake yi wa mutanen kauyen.

Silas kuwa bayan ya ji haushin abin da akayi masa sai ya juya ya dirka wa Captain Mani harsashi shima ya juya ya dirka wa masa harsashi.

Yanzu dai an kwashe gawan su zuwa biriki a Yola.

Share.

game da Author