WAEC 2017: Kashi 26% kacal suka cin darussa 5 har Turanci da Lissafi

0

Kashi 26 bisa bisa 100 na wadanda suka rubuta jarabawar fita sakandare, SSE, ta karshen shekara, suka iya cin darussa 5 har da lissafi da Turaci. Hakan ya nuna irin yadda aka samu mummunan faduwar jarabawa.

Wannan ya sha bamban da kason 28.59 da kuma kashi 38.50 a cikin shekarun 2015 da 2016, a wurin taro a Katsina.

Shugaban Majalisar Ofishin Jarabawar na kasa ya bayyana a lokacin da ya ke fitar da sakamakon jarabawar Nowamba/Disamba.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ya ruwaito Mista Adenipekun ya ce daga cikin mutane 135,945 da suka yi rajistar rubuta jarabawar, 133,223 kadai suka rubuta jarabawar.

Ya kara da cewa daga cikin 133,223 da suka rubuta jarabawa, an fito da sakamakon da kowanen su ya samu.

Amma kuma Adenipekun ya kara da cewa an rike sakamako 1,738, saboda har yanzu ana kokarin tantance wasu sakamakon na su, a dalilin kuskuren kasa gano sunayen masu su, dalilin kuskuren da suka yi wajen cika fam.

A karshe ya ce 34,664 ne kacal daga cikin 133,223 suka iya cin darussa 5 abin da ya yi sama, ciki har da lissafi da Turanci. Wato kashi 26 bisa 100 na wadanda suka rubuta jarabawar kenan.

Share.

game da Author