TSAKANIN MAJALISA DA IGP: “Dole Sujeto janar, Idris Ibrahim ya bayyana a gaban majalisa” – Saraki

0

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya gargadi Sufeto Janar din ‘yan sanda Idris Ibrahim da ya tabbata ya gurfana a gaban kwamitin majalisar da take bukatar sa ya zo ya amsa zargin yin sama da fadi da kudaden gwamnati da wasu laifuffuka da ake masa wanda Sanata Misau ya sanar wa majalisar kuma ya wanke kan sa.

Sanata Misau ya sanar da majalisa cewa sufeto janar din ‘yan sandan ya na da guntun kashi a jikin sa sannan ba mutum bane mai gaskiya.

Idris ya aika da wasika majalisar cewa dalilin da ya sa bai bayyana a gaban kwamitin majalisar ba shine don maganar na kotu.

Saraki ya ce majalisar ba za ta amince da wannan dama da yake dogaro da shi ba domin kuwa doka ta basu daman yi ma sa irin wannan kira.

Kwamitin ta sake aika masa da takardan gaiyata da ya bayyana a mako mai zuwa.

Share.

game da Author