Babban jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya shawarci Shugaba Muahammadu Buhari yadda zai yi amfani da sauran wa’adin zangon san a farko ya kara ciyar da Najeriya gaba.
Tinubu ya yi amfani wata dama da ya samu ne a matsayin sa na mai jawabi wajen kaddamar da littafi mai kunshe da nasarorin da gwamnati Buhari ta samar a cikin shekaru biyu, wanda aka gabatar a dakin taro na Fadar Shuagaban kasa, inda ya ce duk da cewa Bauhari ya yi kokari a shekarun sa biyu na farko, akwai matukar bukatar ya kara zage damtse.
Tinubu ya ce babban abin da Najeriya ke tinkaho da shi, bai wuce danyen man fetur ba, wanda ko ba-jima, ko ba-dade zai kare. Sai ya i roko ga Najeriya da ta karkata tsare-tsaren ta wajen samo wasu hanyoyi na ko-ta-kwana, domin idan fetur ya kare, ana da wasu hanyoyin kenan, ba tare da kasa ta gigita ba.
Daga nan sai ya yi gargadin cewa kada a kuskura a yi wa shawarar da ya ba Buhari a bainar jama’a kallon wata hujjar cewa akwai wani dogon shamaki tsakanin sa da Shugaban Kasa, wanda ya kange su daga ganawa a tsakanin su.
Ya ce duk wanda ya yi wannan tunanin, to tunani ne mai rauni. Kuma duk wanda ya buga labarin cewa akwai dogon shamaki tsakanin sa da Buhari, to ya kwan da sanin cewa labarin bogi ne.
Ya ce idan Buhari na so ya cimma kudirorin sa, to sai ya yi jan aiki sosai a fannin tattalin arziki. Ya kuma yi nuni kan kasafin 2018 da aka gabatar makon da ya wuce da cewa kasafi ne wanda idan aka yi amfani da shi a bisa turbar da a ka tsara, to zai saisaita Najeriya akan turbar da ta dace.
‘Lokaci ya yi da za a fitar da talakawa daga fama da radadin yunwa, zuwa inda za su rika kwana su na tashi da kyakkyawan fatan samun yalwa a kullum.”
Ya ce a matsayin Najeriya daya daga cikin kasashen da suka fi yawan al’umma a duniya, bai yiwuwa a ce ta taka tudun-mun-tsira ba tare da kafa manyan masana’antu a cikin kasar ba.
”Kasashen da suka ci gaba irin su Ingila, Japan da China duk sai da suka fito da tsare-tsaren bai wa masana’antu kariya, suka fifita tare da kwadaita samar wa jama’a ayyuka, kuma suka yawaita kayan da suke fitarwa ana sayarwa kasashen waje.
Daga nan sai ya ce ya kamata a rika aiwatar da maganganun da ake yi na kawo sauyin inganta masana’antu a Najeriya, ba kawai a bar batun ana ta hauragiya a fatar baki kwai ba.