Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa biyan kudin wuta da tsada a Nijeriya ya zama wajibi, domin babu wani tsimi ko dabarar da gwamnati za ta yi, sai dai a sha lantarki da tsada kawai.
Osinbajo ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke bayani a Taron Masana Harkokin Kasuwanci na Shugaban Kasa, a Fadar sa da ke Ahia, ranar.
Laolu Akande, wanda ya yi magana a madadin mataimakin, ya ce amma a halin da ake ciki, abin da gwamnati kawai za ta iya yi shi ne ta daure ba ta kara kudin lantarki ba a yanzu.
“Abin da mu ke kokarinn yi shi ne kada mu kara farashin kudin harken lantarki a yanzu tukunna.”