Tilas Najeriya ta ci gaba da neman danyen mai a Arewa-maso-gabas – Minista Kachukwu

0

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ibe Kachukwu, ya bayyana cewa tilas sai Najeriya ta ci gaba da neman danyen man fetur a yankin Arewa maso gabas domin kara wa daben tattalin arzikin ta makuba.

Kachukwu ya bayyana haka ne a jiya Talata yayin da aka taron nazarin kasafin kudi na 2018, a Abuja.

Ya kara da cewa “wajibin mu ne a matsayin mu na kasa mu ci gaba da jan aikin hako danyen mai a a ko’ina ne cikin fadin kasar nan. Hakan kuma bai hana aikin hako danyen mai da ake yi ba a yankin Neja-Delta.”

“Ko da yaushe a yankin muna hako danyen mai a duk inda muka same shi, kuma kudin shigar da muka kiyasta samu daga danyen man fetur, a kasafin 2018, kashi 60 ce kawai daga cikin kashi 100 na kudaden shigar da Nijeriya ke sa ran samu a wannan kasafin na 2018.

“Don haka akwai matukar bukatar ci gaba da hakar danyen mai ko a ina ne, matsawar mu na da yakinin samun sa a yankin.

Daga nan sai Kachuku ya kara da cewa a tsarin sa, ba NNPC ne kadai zai rika nemo danyen mai a yankin Arewa maso gabas ba, gwamnati na kokarin jawo kamfanoni masu zaman kan su su shigo cikin aikin neman danyen man fetur a yankin.

A wurin taron ita ma Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ta ce tilas sai kasar nan ta farfado da tsarin biyan haraji domin tattalin arzikin mu ya kara inganta.

Ministar ta yi bayanin cewa daga cikin mutane milyan 69 a Najeriya wadanda ke aiki, milyan 14 kadai ne ke biyan haraji.

“Yawancin masu biyan haraji ma’aikatan gwamnati ne da kuma masu aiki a kamfanoni masu zaman kan su. Amma game-garin mutane ba su biya, ko kuma ba su biyan adadin da ya kamata su biya.

Ta kara da cewa cikin 2018 gwamnatin tarayya za ta tabbatar an kididdige duk sauran wadanda ba su biyan haraji, za ta tattara adadin su a tabbatar su na biya.

Share.

game da Author