• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    Dino Melaye

    Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa mutane hari a jihar Neja – SSG

    Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 11 a Zamfara a karshen makon jiya

    SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

    SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

    Askarawan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 42, sun kama 20 sannan sun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su – DHQ

    Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru

    Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

TATTAUNAWA: Gwamnatin APC, ta PDP ce – Sule Lamido

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
November 3, 2017
in Rahotanni
0
Sule Lamido

Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa SULE LAMIDO ya bayyana aniyar sa ta neman tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019. Bayan ya sanar wa jam’iyyar sa wannan muradi na sa a rubuce, Lamido ya yi Tattaunawa Ta Musamman da PREMIUM TIMES HAUSA, inda ya yi bayani dangane da batutuwa da dama. A sha karatu lafiya.

PTH: Kamar makonni biyu da su ka gabata ka rubuta wa manya da kananan magoya bayan jam’iyyar ku ta PDP wasika, inda ka bayyana musu halin da kasar nan ke ciki, tare da nusasshe su cewa tilas PDP ta mike tsaye domin ta ceto kasar nan. A cikin wasikar kuma har ka gabatar da kan ka, a gare su ka na mai neman amincewar su a matsayin dan takarar PDP na zaben shugaban kasa a 2019. Me ya sa ka cimma wannan matsaya?

LAMIDO: To ai ka san jam’iyyar siyasa dai a Afrika ta na samun karfin ikon ta da karsashin ta ne daga dimbin magoya bayan ta. Ni a tsarin koyarwar siyasar da na samu, a tsarin alkiblar siyasa ta, kowane dan jam’iyya, ko ma a wane lungu ya ke, ya na da tasiri sosai a cikin jam’iyya. Duk wata rawar gaban hantsi ko bugun gaba da jam’iyya za ta yi, to bimbin magoya bayan ta din nan su ne abin alfaharin ta, kuma da bazar su ta ke rawa.

Dalili kenan na ce musu na fito domin su goya min baya, mu fitar da Nijeriya daga wannan tsarin siyasar ‘yar karma-karma, siyasar dora wa jama’a karan-tsana, siyasar ‘yan damaga, kuma siyasar cusa tsoro a zukatan al’umma.

Ka ga kenan a irin wannan tafiya tun da farko sai mun fara sanar da mgoya bayan mu da ba su gajiyawa ko sarewa komin wuya komin dadi. Wannan na nufin duk wani dan jam’iyyar PDP sai mun sanar da shi cewa ina so zan fito takara a zaben 2019.

Wannan wasika da na rubuta na aika, tamkar wani dan kwarya-kwaryar lamari ne na cikin gida, inda na gabatar da kai na ga ‘yan gidan mu kenan zan ce. Idan har su ka ga cewa na cancanta, to za su iya wakilta ni. Saboda na yi amanna da cewa dukkan damuwar da mu ke da ita a kan matsalolin kasar nan, duk iri daya ce. Kuma irin hanyoyi daya mu ke hangowa a matsayin mafitar mu ta kaiwa ga tudun-mun-tsira.

Watau idan aka yi duba da irin yadda al’amarin kasar nan ke tafiya, jam’iyyar APC fa ba za ta iya hada kan Nijeriya ba. Ba wai adawa ce na ke kokarin nunawa ba, amma idan ka yi nazarin abin da ke faruwa a Nijeriya daga shekaru uku zuwa yau, za ka kara fahimtar cewa akwai damuwa a zukatan ‘yan Nijeriya.

To ina kuma ina sane da cewa akwai wadanda nan gaba za su fito su ce su na neman takara kamar yadda a yanzu na fito. Amma dai ya na da muhimmanci mu san cewa duk ma abin da za mu yi to mu yi kokarin dawo da kima da darajar jam’iyya. Kuma mu sa kishin Nijeriya a farko shi ne gaba da komai a wannan siyasa. A karshe, duk ma wanda zai kasance shi ne dan takarar da jam’iyya za ta tsaida, bayan an yi zaben fidda-gwani, to ya kasance dan PDP ne na halak malak, wanda ya san PDP, kuma wanda ‘yan PDP su ka sani, ba dan taka-haye ba.

Idan mu ka yi hakan, to PDP za ta iya tunkarar ‘yan Nijeriya cike da alfaharin cewa ga wannan shi ne dan takarar mu, kuma mun gamsu da cewa mun ba ku dan takara nagari, mai inganci. Saboda na sha cewa ko dai mu tsaya mu yi abin da ya dace mu yi a tsarin yadda ya dace a yi shi, ko kuma idan 2019 ta zo, to Nijeriya na iya afkawa cikin babbar matsala. Jam’iyyar PDP ita kadai ce jam’iyyar da za ta iya nada gammo ta dauki dutsen Dala, saboda ita ce jam’iyya mai kimtsi, mai tushen siyasa, mai kaunar hadin kan Nijeriya.

Ku dubi irin yadda aka kafa jam’iyyar, ba daga sama a rana daya ta fado ba, sai da aka sha rana aka sha wahala kafin a kafa ta.

PTH: Ka na daya daga cikin wadanda su ka kafa PDP. Shin ko akwai wani abin boye da ba mu sani ba, dangane da gwagwarmayar da ku ka yi kafin kafa PDP?

LAMIDO: Ba na jin akwai wani abin da jama’a ba su sani ba.

PTH: Wasu daga cikin mambobin jam’iyyar PDP wadanda su ka fusata, su ka fice daga jam’iyyar an ce su na kokarin dawowa PDP. Amma yawanci masu son dawowar, masu bukatar tsayawa takarar shugabancin kasar nan ne. Har mun ma ji ana rade-radin cewa Atiku ya ce zai dawo PDP, matsawar za a ba shi takara. Me ka ke tunani a kan haka?

LAMIDO: Duba nan, a lokacin da su ka fice daga jam’iyyar, tabbas akwai damuwa a cikin PDP. To wannan damuwar ai wasu gwamnoni bakwai sun yi tsokaci da gargadi a kan ta, su ka nuna cewa akwai fa matsala a cikin PDP. Ganin haka, mun tashi mu ka yi zagaye mu na bin manyan kasar nan, idan za ka iya tunawa. Duk mu ka shaida wa shugabannin mu kamar su Cif Olusegun Obasanjo, Alex Ekweme, TY Danjuma, Shehu Shagari, Babangida da sauran su.

Mu ka nuna musu cewa abin da jam’iyyar PDP fa ke ciki idan ba a yi gaggawar daukar mataki ba, to nan gaba Nijeriya za ta iya afkawa cikin rudani da matsala ta tsaro. Mu ka ce musu wannan matsala ta wuce matsalar cikin gida ta PDP fa.

A lokacin da Bamanga Tukur ke mulki, ya kamata a ce PDP na yin taro akai-akai, amma aka shafe shekara daya Bamanga bai kira taro ba. To ka ga kenan idan jam’iyya ba ta tafi a kan turba ba, akwai matsala, gwamnati ce ke da asara, tunda ita ce jam’iyya mai mulki ta kafa.

Bayan an sha sa-toka-sa-katsi, wasu su ka fice daga jam’iyyar. Mu ka rasa gwamnoni biyar, mu ka rasa ‘yan majalisar dattawa da na tarayya wadanda duk su ka shiga wata jam’iyya.

To, yanzu da su ka koma can, me aka tsinana musu? Sun samu kwanciyar hankali? An yi musu sakayya? Sun tsira daga abin da su ke gudu? Idan sun dawo, to dama ba sabon abu ba ne, sun dawo cikin jam’iyyar da su ka bari. Dama ai PDP ce gidan su, amma APC ai gidan haya ce ko shekar tsuntsaye, ba gidan zama ba ce. Shi gidan haya kuwa zaman a-taru-a-kwana ake yi, ba zaman-dirshan ba.

Tun daga Atiku da Saraki da ma kowane a cikin su duk mu na yi musu lale marhabin idan su ka dawo. Dama na mu ne, ‘yan PDP, duk inda su ka shiga, to akwai jinin PDP a jikin su. Duk nisan gudun da mutum zai yi, ai ba zai iya tsere wa ran sa ba.

Dangane da batun kafa sharuddan dawowar Atiku kuwa, ba na jin akwai wasu sharudda. To wane ne ya gindaya sharuddan? Yaushe aka gindaya su? Kai, babu wasu sharudda. Idan sun dawo dai za mu karbe su hannu bibbiyu, tunda za su dawo inda su ka fi kauna, inda aka fi daukar su da daraja da mutunci, kuma inda su ka zama yadda su ke a yau.

Amma a halin da su ke yanzu, kowa ya san sun zama mujiya a cikin tsuntsaye. Yau a ci mutuncin su, gobe tozarta su, jibi a ce musu barayi. A ce PDP jam’iyyar barayi a gaban su, kuma ba su iya tankawa ko su kare kan su. An jima ka ji Lai ya ce ba su da kunya, kuma su na kallo ana yi musu wannan cin-fuska.

To su je su yi ta jifar mu da kowane irin mummunan kalami. Abin da kowa ya sani dai shi ne, PDP ce ta kafa gwamnatin APC. Gwamnatin APC dai ta mu ce mu ‘yan PDP.

PTH: A matsayin ka na dan Nijeriya, ko ka na damuwa da irin halin da gwamnatin Buhari ke ciki? Za ka iya cewa abin takaici ne, kamar yadda wasu ke korafi, ko kuwa za ka ce kai gaba ta kai ka, a matsayin ka na dan adawar da idan aka amince maka kai ne za ka kara da shi a zaben 2019?

LAMIDO: Wato ka lura da wani abu, a matsayina na dan Nijeriya, a gaskiya ba na murna da irin shirmen da gwamnatin Buhari ke tafkawa. Ko na ce gwamnatin APC. An ba su nauyin jagorancin jama’a, amma abin bakin ciki kawai shi ne, sun samu mulki da rana tsaka, alhali ba su shirya ba, kuma ba su da wani shiri a lokacin.

Saboda ba su shirya ba fa shi ya sa su ke biye su na shirga karairayi domin su lullube shirmen da su ke tafkawa. A lokacin da su ke kamfen, ba su komai sai jifar PDP da kazafin cewa ita ce Boko Haram, sun yi ta ce mana shaidanu, su na muzanta mu. To a yanzu da gwamnati ke hannun su, sun kasa farkawa daga barcin tunanin cewa har yanzu dabi’un su na ‘yan adawa ne masu neman mulki, sun kasa gane cewa a yansu mulkin a hannun su ya ke.

Saboda fa kwakwalwar su a toshe ta ke, ba su kuma da sanin makamar-akalar-gwamnati, sai su ke ta yada farfaganda daya. Sannan kuma idan ka yi magana a kan wani shirme da bulkarar da gwamnatin su ke tabkawa, a matsayin ka na dan Nijeriya, sai su rika muzanta ka. Ka ga akwai hadari a ce gwamnati ce ke muzanta dan Nijeriya idan ya koka dangane da ita.

Yau a Nijeriya sai mutanen gwamnati su rika muzanta ‘yan Nijeriya, idan su ka bayyana ra’ayin su dangane da yadda gwamnati ke nunke su baibai. Idan ka yi korafi sai su ce maka sarkin korafi. To wai idan ka na korafi dangane da abin da aka yi maka na ba daidai ba, kamata ya yi gwamnati ta tambaye ka, me ya sa ka ke raki. Maimakon haka, sai a fara shaguben ka ana cewa sarkin raki.

Shin idan ‘ya’yan ka na kuka saboda su na jin yunwa, ya za ka yi da su? Za ka fita ka nemo musu abinci ne, ko kuwa za ka rika yi musu fada ka na cewa sun cika raki?

Ai wato mutanen wannan gwamnatin ba su da tunani, ba su san abin da ake nufi da shugabanci ba. Sun hau shugabanci ne kawai a bagas, sai su ke kallon mulkin kamar wani gadon gidan su. An wayi gari wadanda ba su taba tsinana wa kasar nan komai ba, ba su ma san yadda aka sha wahalar ririta siyasar kasar ba, yau sun shiga rigar mulki su ne masu cewa a yi ko a bari.

Ka dub aka gani, lokacin da Shugaba Buhari ba shi da lafiya har aka tafi da shi waje, sai Lai da Adesina su ka rika cewa wai ya na dai can kwance ne ya na shan magunguna kawai. Amma lafiyar sa kalau. Amma lokacin da ya dawo, sai ya ce ai ya sha fama da rashin lafiya. To mene ne abin boyewa ga rashin lafiya? Buharin nan fa ba na Lai ko Adesina kadai ba ne su biyu.

Lokacin da ‘Yar’Adua ba shi da lafiya, su Lai ne fa a sahun gaban masu cewa sai an bayyana rashin lafiyar sa. Har cewa su ke yi su na da ‘yancin su san hatta yadda shugaban kasa ke shan ruwa. To yanzu ga su rike da ragamar shugabanci, mu na ta shan mamakin irin tulin karairayin da su ke kantara mana.

Ka dubi batun harkallar bilyoyin dalolin kamfanin NNPC. Hakan ta faru a daidai lokacin da yajin aiki ya zama ruwan dare a kasar nan. Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa da sauran kungiyoyi su na ta yajin aiki saboda gwamnati ta ki kula su ko ta ki cika musu alkawurran su. Idan ka dauki dala milyan daya ka zuba wa jami’o’i, za ta magance matsalar su. Haka idan ka dauki wasu daga kudin ka magance matsalar Kungiyar Likitoci ta Nijeriya. Ga manyan titinan kasar nan sun ragargaje. Idan ka zuba kudi a bangaren titina, za ka warware wata matsalar. Amma dubi titin Kaduna zuwa Kano. Haba jama’a!

Aka zo aka ce Asibitin Fadar Shuagaban Kasa babu ko sirinji. Matar shugaban kasa ce da kan ta ta fadi haka fa, bayan an ce an ware masa kasafin naira bilyan uku. Maimakon su gaggauta kai magani, sai aka rika cewa mun cika raki. To Alhadu Lillahi, a yau har Aisha na cikin masu raki da kukan cewa ana ba daidai ba a gwamnatin Buhari. Ita kan ta APC din ta fara raki. Ka ga Nijeriya ta zama kasar masu raki kenan.

PTH: Gangamin taron PDP ya kusa, amma kuma akwai korafe-korafe da shari’un da aka rika fama da su dangane da wanda zai zama shuagaaban jam’iyya. Shin hakan na nufin a yanzu kun kuwa dauki wani darasi kenan?

LAMIDO: To ka na ganin dai mun kusa shiga shekarar da za a sake zabe. Duk ma wanda za a zaba ya zama shugaba, ba zai zama wani mai karfin ikon yin karfa-karfa ko banga-banga ba. Ba kuma zai iya tirsasa wakilan zabe daga Neja ko Sokoto ko Jigawa da sauran jihohi ba, ya ce ga wanda ya ke so a zaba, kuma su bi son ran sa.

Yanzu mun kai wani matakin da babu wani da zai yi wa saura banga-banga, ko ya maida harkar jam’iyya ta sa ce kan sa. Duk ma wanda zai zama shugaban jam’iyya tilas sai ya dogara kuma ya nemi goyon baya da gudummawar ‘yan jam’iyya domin ya cimma nasara.

PTH: Daya daga cikin manyan kalubalen da wanda zai zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, shi ne yadda zai maido da akalar tattalin arzikin kasar nan a kan turba. Yanzu ga shi dalar Amurka ta yi tsayuwar-gwamin-jaki a wuri daya. Litar man fetur ta tsaya a naira 145, babu maganar samun rangwame. To ya ka ke….

LAMIDO: (Ya katse tambayar): Ashafa wannan duk wani bayani ne ka ke yi mai zurfi ko mai kama da lissafin-dawakan-Rano. Ita fa kwakwalwar dan Adam dama can an yi ta ne domin ta tunkari kalubale. Na ga kasashe da yawa wadanda ba su da komai a da can, daga baya kuma sun zama hamshakai. Abin fa ya dogara ne, ga kyakkywan tunanin bullo da hanyoyi mafita. Ba wai kawai surutai ba ne abin ko wani kame-kame. Kasashe da dama ba su da kayan kera abubuwa, babu albarkatun kasa, amma sun kokarta sun zama manyan kasashen da ake tutiya da su a yau. Ai sai ka na da basirar yin tunanin kawo ci gaba sannan za ka iya ci gaba.

Ga Koriya ta Kudu nan, su ne a sahun gaban kasashe masu gina manyan jiragen ruwa, amma kuma ba su da kayan hadin kera jiragen ruwa a kasar su.

Amma mu kuma a nan, wannan gwamnati wacce idan ta yi ba daidai ba ka yi magana sai ta ce ka cika raki, gwamnatin da ta raba kan ‘yan Nijeriya, ba s da wani tunani ko basirar iya fidda kitse daga wuta. A cikin shekara biyu da rabi da su ka gabata zuwa yau, kamfanoni nawa ne daga kasashen waje su ka shigo Nijeiya su ka zuba wani abin kirki da sunan jari a cikin kasar nan? Babu! Ta yaya za su iya tabuka wani abin kirki? Ku dubi Angola kuma ku dubi yadda ake zuba dimbin jari a cikin kasar. Ga Masar nan a yanzu ta na bugun gaba da tinkaho da karfin tattalin arzikin ta. Ga kuma kananan kasashe irin su Rwanda. Don haka duk yadda z aka cika mutane da surutai da dadin zance, idan ba ka da basira fa ba za ka iya saisaita Nijeriya a kan turba ba.

Nan aka wayi gari daya daga cikin mashawartan Buhari mai suna Farfesa Itse Sagey ya ce jam’iyyar APC garken barayi ce, garken mahandama ce. Kuma ya na cikin gwamnatin ta APC. Shin ta yaya masu zuba jari daga kasashen waje za su amince su shigo su zuba jari a Nijeriya?

PTH: Duk lokacin da ba ka Kano, in dai ba Abuja ka dan leka ba, to ka na can kauyen ku Bamaina a jihar Jigawa ka yi zaman ka. Shin me ke ba mutum kamar ka sha’awa da rayuwar kauye ne?

LAMIDO: Mahaifi na da mahaifiya ta duk a kauye aka haife su, ni ma a can su ka haife ni. Duk irin matsayin da na kai ko wanda zan kai, ko da shugaban duniya zan zama idan ma ana yin shugaban duniya din, to kauye dai can ne tushe da asali na. Rayuwa ta daga kauye ta fara, dalili kenan na ke kauna da sha’awar zaman karkara fiye ma da tunanin ka.

Tags: AbujaAPCBuhariHausaHausa Premium TimesJigawaLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMESsule lamido
Previous Post

Abubuwa 5 da El-Rufai zai yi da bashin dala miliyan 350

Next Post

Ba za mu dawo da Abdulmumini ba sai ya roki majalisa – Majalisar Wakilai

Next Post
Na yi nadamar maganganun da nayi akan Buhari – Abdulmumini Jibrin

Ba za mu dawo da Abdulmumini ba sai ya roki majalisa - Majalisar Wakilai

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • AN YANKA TA TASHI: A biya ni naira miliyan 21 kuɗin fom ɗin takarar gwamna da na siya a PDP – Ɗan takarar gwamna
  • ZARGIN ƘARFA-ƘARFA A SIYASAR ENUGU: Sanata Ekweremadu ya saka takalmin ficewa daga PDP zuwa APC
  • TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’
  • KATSINA TA DAGULE: An bindige manoma 12 a gona, an sace ‘limaman’ Cocin Katolika biyu da yara biyu
  • Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.