TAMBAYA: Malam menene hukuncin rina farin gashin kai ga musulmi don kwalliya? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Malam menene hukuncin rina farin gashin kai ga musulmi don kwalliya?

AMSA:Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Rina farin gashin kai da gemu lamarin ne da magabata suka yi sabani kamar haka:

1) Haramci: mafi yawa daga cikin malamai sun haramta rina gashi da sinadarin man gashin da ke rina gashi zuwa baki. A gurin wasu malaman haramcin yahada maza da mata baki daya.

Amma wasu daga cikin malamai sunada ra’ayin halarcin rina gashi da sinadarin man gashin da ke rina gashi zuwa baki ga mata kawai. Domin su ‘yan kwaliya ne, kuma haramcin ya tsaya ga maza ne kawai a gurinsu.

2) Karhanci: Manyan malamai da suka yi bincike akan hadisan da suka rahamta rina gashi zuwa baki, sun tafi ne akan cewa makaruhi ne rina gashi zuwa baki. Kuma sukace hadisan da suke dauke da haramcin hakan akwai cece-kuce tsakanin malamai wajin ingancinsu da manufansu, sabo da haka ne ma suke ganin rashin haramcinsa shi ne zance mafi adalci acikin rina gashi.

Masu wannan fihimtar sun tabbatar da cewa Sahaban Annabi (SAW) kamar Hasan, Husain, Usman, Sa’ad da sauran magabata duk suna rina gashin su da sinadarin rina gashi mai baki, wanda hakan yake nuna halarcin rina gashi zuwa baki.

3) Sunnanci: Sunna ne rina gashi da sinadarin man gashin da ke rina gashi zuwa kalar da ba baki ba ne. Abu Huraira ya ruwaito fadin Annabi SAW “ Yahudu da Nasara basu rina gashin su, to, ku sabamusu. Buhari da Muslim.

Rina farin gashi zuwa wani kalar da ba baki ba ne yana daga cikin sunnan musulunci.

Allah ya sa mucika da Imani. Amin.

Share.

game da Author