Bayan sanar da nade-naden da Buhari ya yi don karyata rahoton jaridar Business Day da Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar yada Labarai Femi Adesina ya yi, PREMIUM TIMES ta bi diddigi wadannan sunaye da fadar shugaban kasa ta wallafa in da ta gano cewa kusan rabin wadanda aka nada babu sunayen su a ciki.
Ga wadanda muka gano kamar haka:
Babu sunayen shugaban gidan rediyo da na talabijin na Tarayya
Shugaban gidan rediyon Tarayya Mansur Liman Wanda dan asalin garin Daura ne ba ya cikin sunayen.
Yakubu Ibn Muhammed, daga jihar Bauchi ma ba sunan sa. Shine shugaban gidan talabijin na Tarayya.
Babu sunan Ismael Ahmed
Ismael Ahmed Mai taimaka wa shugaban kasa Kan ‘Social Investment Programmes’ a ofishin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo. Ismael Ahmed dan jihar Kano ne.
Sauran masu bada shawara SSA da babu sunayen su sun hada da
Ibrahim Bapetel Hassan, daga jihar Adamawa, Tolu Ogunlesi, Lauretta Onochie, da Shaban Sharada.
Akwai kuma Nasir Saidu Adhama, Abdulrahman Bappa Yola, da Bashir Ahmed, Wanda ‘yan asalin jihar Kano ne.
Akwai wasu shugabannin ma’aikatu da aka nada da babu sunayen su a jerin sunayen kamar haka:
Joseph Ari, shugaban ma’aikatar ‘ Industrial Training Fund’ Simbi Wabote na ‘ Nigerian Content Monitoring Board’ ; Aboloma Anthony na ‘ Standards Organisation of Nigeria, Mamman Amadu, na ‘Bureau of Public Procurement’ Ahmed Bobboi, ‘ Petroleum Equalization Fund’ da Sa’adiya Faruq, kwamishina a ‘National Commission for Refugees, Migrants and Internally Displaced Persons.’
Shima Abubakar Bello na NEXIM, babu sunan sa
A ma’aikatar Kiwon Lafiya ma akwai sunaye kamar haka da ba da cikin sunayen da gwamnati ta lissafo.
Babu sunayen Babatunde Salako, na ‘National Institute for Medical Research’ daga jihar Ogun; da Chikwe Ihekweazu, na ‘ ‘National Centre for Disease Control’ duk an nada su ne a 2016.
Bayan haka akwai Echezona Ezeanolue na ‘National Primary Healthcare Development Agency; Usman Yusuf, na ‘National Health Insurance Scheme’ da Sani Aliyu na, ‘National Agency for the Control of AIDS.
Sauran sun hada da;
Nurudeen Rafindadi na NEMA da ga jihar Katsina; shugaban FCT IRS Abdullahi Attah; da Bayo Somefun, shugaban ‘Nigeria Social Insurance Trust Fund.’
Akwai , Luci Ajayi, na ‘Lagos International Trade Fair Management Board; da Emmanuel Jimme, Managing na ‘Nigeria Export Processing Zones Authority.’
Akwai wadanda nada da ba a rubuta sunayen su daidai ba, wasu Kuma an saka su a wasu ma’aikatan da ba nan suke ba.
Da muka nemi ji daga bakin Femi Adesina ko menene dalilin yin hakan, ya ce ba su rubuta sunayen duka wadanda aka nada bane saboda suna da Shirin yin haka nan gaba.