Ministan tsaro Mansur Dan-Ali ya ce dakarun sojin Najeriya za ta fara wani atisaye da ake kira ‘Operation Harbin Kunama’ a jihar Zamfara a watan Disemba.
Ya fadi haka ne da yake hira da manema labarai a garin Gusau.
Mansur Dan-Ali ya ce kamar yadda sojoji ke yin irin wannan atisaye mai suna ‘Operation Awatse’ a yankin kudu maso yamma da ‘Operation Crocodile Smile II’ a yankin kudu maso kudu’ za ta yi ‘Operation Harbin Kunama’ a jihar Zamfara.