Saleh ya fadi haka ne a taron karrama wa da bada kyautuka ga wadanda suka sami nasara a gasar rubuta gajeruwar labari da akayi a Otel din Sheraton dake Abuja.
A shekarar bara ne BBC ta sanar da gasar “Hikayata” ga marubuta mata su fafata.
” Har yanzu marubuta mata na gaba da maza wajen rubuta labari masu ban al’ajabi da sa mai karatu nazari.
Saleh ya Kara da cewa BBC ta kirkiro irin wannan gasa me domin kara wa mata karfin guiwa yin rubutu. Sannan kuma
Aisha Sabitu ne ta zo na daya da labarin ta Sansanin ‘Yan Gudun Hijira a gasar na shekarar bara.
” Sama da marubuta 400 ne suka aiko da labaran su daga ko ina a fadin duniya. Hakan nuni ne cewa gasar ta karbu. Duk da cewa kafin a fidda wadanda suka yi nasara sai da aka jigata saboda kyan sauran a wajen tantancewa.
Saleh ya gode wa alkalan da suka yi aikin da ya hada da Balaraba Yakubu, Rahma Abdulmajid da Ibrahim Malumfashi.
Maimuna Sani Beli daga jihar Kano ce ta lashe gasar da labarin ta mai suna ‘Bai Kai Zuci ba’
Balkisu Sani Makaranta, ne ta zo na biyu, Inda Habiba Abubakar da Hindatu Samai’ila Nabame suka zo na uku tare.
Sauran manyan bakin da suka halarci bukin sun hada da kakakin majalisar Wakilai Abdulrazak Namdas, shugaban gidan rediyon Tarayya, Mansur Liman da Ramatu Tijjani.
Discussion about this post