Shirya fim da harshen Turanci zai sa mu da’da samun karbuwa a duniya – Fati SU

0

Fitacciyar jaruma ‘yar wasan Hausa, Fati SU Garba ta yaba wa kokarin da masu shirya finafinan Kannywood suke yi na shirya fim da harshen Turanci.

Da take tattaunawa da PREMIUM TIMES Fati SU tace wannan kokari ya cancanci yabo.

” Idan aka yi la’akari da yadda aka samu ci gaba a duniyar finafinan Hausa da irin yawàn masoyan mu da ya hada da Wadanda ma ba su jin harshen Hausa, yin haka zai sa mu dada samun Karbuwa a wajen mutanen da ba ‘yan Arewa ba kawai.

Fati dai tayi digirinta ne a fannin aikin gwamnati da harka da jama’a ajihar Neja.

Bayan haka ta Zama zakaran gwajin dafi a harkar finafinan Kannywood.

Tana daga cikin jaruman da suka burge a fim din ‘ There is a Way da Kuma ci gaban sa ” This is the way” Wanda zai a fara nuna Shi a sinima a Disamba.

Da aka tambaye ta ” Maimakon mai da hankalin wajen shirya finafinan a harshen turanci me ya sa ba a gyara na Hausa da suke yi ba da yi masa fassara Mai kyau kamar yadda finafinan India da suke koyi da, suke yi Kuma har cin kyautuka suke yi har a kasashen Amurka, Fati ta ce, ” Wannan bayani da kayi gaskiya ne amma babu laifi don mun yi fim da harshen turanci. Hakan da muka fara yi yanzu nuni ne ga mutane cewa muma fa ba a bar mu a baya ba a harshen Turanci.

” Idan Ka duba yanzu ana saka fannin finafinan Kannywood a gasar kyautukar finafinan na duniya. Kwanan nan Jarumi Ali Nuhu da wadansu abokanan aikin mu suka dawo daga Kasar Britaniya Inda suka lashe kyautuka.

” Saboda haka wannan abu da muka fara abu ne mai kyau Kuma sannu a hankali zamu kai ga nasara.

Daga karshe Fati ta jinjina wa jaridar PREMIUM TIMES da na Hausan ta wato PREMIUM TIMES HAUSA da irin gudunmuwar da suke ba farfajiyar finafinan Kannywood wajen yada labaran ta.

Share.

game da Author