Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kaddamar da bankin Inshora na Musulunci na farko a Nijeriya, wanda ake kira da suna Jaiz Takaful Insurance.’
A wurin kaddamar da inshorar, Sarkin na Kano ya bayyana cewa shigo da wannan tsari a Najeriya abin alheri ne matukar gaske, musamman domin za ta taimaka wajen habbaka tattalin arzikin kasa.
Ya ce wannan tsari zai tafi ne a bisa tsari na shari’ar musulunci, kuma ba wai sai musulmi ne kadai zai iya amfana da shi ba. Ya ce kowane addini mutum ya ke yi zai iya cin moriyar tsarin matukar dai ya shiga yay i rajistar kaya ko kadarorin sa.
“Wannan tsari na inshora zai taimaka wa masu kananan masana’antu, ya rama musu dukiyoyin su, musamman idan wani ibtila’i na asara ya afka wa kadarorin mutum. Amma fa ba addu’a ake yi hakan ta farun ba.
Daga nan sai ya yi kira ga daukacin jihohi musamman na Arewacin kasar nan da su yi rajistar dukkan kadarorin su, musamman ababen hawa, gidaje da sauran su a tsarin Takaful.
Manajan Daraktan Kamfanin Inshorar Jaiz a Najeriya, Momodou Musa, ya ce za su tafiyar da shirin a bisa tsari na addinin Musulunci.
Shi ma Shugaban Hukumar Gudanarwar Jaiz, Umar Mutallib ya bayyana muhimmancin irin wannan tsari na Takaful.
” Ba kamar yadda yake a sauran kamfanonin Inshora na kasa inda masu zuba kudi ba su da iko akan shirin, wannan shiri kowa da na iko akan harkar.”