Sama da mutane 16, 000 sun mika takardun neman aikin malunta a Kaduna

0

Dalilin kira da gwamnatin jihar Kaduna tayi na wadanda suka cancanta su mika takardun kammala karatun su na NCE da Digiri domin daukar su malaman makarantun Firamare a jihar, daruruwan mutane suna ta kai takardun shaidar kammala karatunsu hukumar SUBEB a jihar.

Zuwa Alhamis 9 ga watan 11, mutane sama da 16,000 ne suka mika takardun su na neman aikin, cewar shafin gwamnatin jihar na tiwita.

Gwamnatin jihar za ta dauki malamai 25,000 domin maye gurbin wadanda suka fadi gwajin da tayi wa malaman makarantun da malamai 20,000 suka kasa cin kashi 75 bisa 100 na jarabawar.

Kungiyar Kwadago da na malamai sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewa da shirin sallamar malamai da gwamnatin take yi. Kungiyoyin sun ce za su shiga yajin aiki na bai daya a jihar daga ranar 23 ga watan Nuwamba idan har gwamnatin jihar bata janye wannan shawara ba.

Share.

game da Author