Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da bullowar wata cuta da ba a san ko wace iri ba ce.
Jami’i a ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Abas Aliyu ya ce mutane uku sun rasa rayukan su a asibitin Usman Danfodio sanadiyyar kamuwa da wannan cuta.
Ya ce likitoci a asibitin sun ce sun ga alamun cutar zazzabin cizon sauro, farfadiya da zuban jini ta idanu a jikin wadanda suka kamu da cutar.
“Duk da haka ba a tabbatar da irin cutar da mutanen suka kamu da shi ba domin an birne su ranan da suka mutu.”
Daga karshe Aliyu ya ce sun aika da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiyan da za su gudanar da bincike kan cutar.