A yau Labara ne kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken harkallar yadda aka yi asarkalar maida Abdulrashid Maina kan aikin sa ya ci gaba da zaman sa a majalisar tarayya.
Cikin wadanda aka gayyata kuma suka halarci zaman domin su bayar da bayanin abin da suka sani da wanda su ka aikata, sun hada da:
Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Shugaban Riko na EFCC, Ibrahim Magu, Ministar Kudi, Kemi Adeosun, da kuma Akanta Janar na Kasa, Ahmed Idris. Sauran sun hada Babban Kwanturola na Hukumar Shige-da-fice, Mohammed Babandede da kuma Babban Sakatare na Ma’aikatar Cikin Gida, Abubakar Magaji.
Dukkan wadanda aka gayyata din sun sha ruwan tambayoyi daga kwamitin, musamman daga shi shugaban kwamitin, Hon. Ali Madakin Gini, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Dala daga Jihar Kano.
An yi jula-jula yayin da kowace hukuma ko ma’aikata ta yi ta kokarin wanke kanta daga zargin ita ke da alhaki wajen asarkalar Maina.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo yadda ta kaya a zaman kwamitin, domin masu karatu su karanta dalla-dalla:
1 – BA DA SANIN OFISHI NA AKA DAWO DA MAINA, inji Winefried Oyo-Ita
Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Winifred Oyo-Ita ta kara jaddada matsayin ta da jajircewa a kan cewa ba da sanin ofishin ta ba ne aka maida tsohon shugaban kwamitin kwato kudaden fanshon da ma’aikata su ka sace, Abdulrashid Maina kan aikin sa ba.
“Ba gaskiya ba ne da Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Abubakar Magaji ya ce daga ofishi na ne umarnin a maida Maina kan aikin sa ya fito.”
“ A bisa tsari, idan za a maida ma’aikaci kan aikin sa, to Hukumar Kula da Daukar Ma’aikata za ta rubuto wasika ga Shugaban Ma’aikata na Tarayya.
“To amma ita Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ba ta tsaya jiran umarnin maida Maina ba, kawai sai ta yi azarbabin maida shi kan aikin gwamnati.” Inji ta.
Ta ce ita dai a matsayin ta na Shugabar Ma’aikata, Maina ba ya cikin ma’aikatan kasar nan, domin ofishin ta bai ba shi takardar sake kama aiki ba.
2 – AN CE MU MAIDA SHI, AMMA BA MU BA SHI WANI AIKI BA, inji Ma’aikatar Cikin Gida
Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Abubakar Magaji, ya bayyana cewa daga Hukumar Kula da Daukar Ma’aikata ta Tarayya takardar maida Maina cikin gwamnati ta fito.
“An turo min kwafen wasikar domin na cika-aiki. To ko sun bai wa Maina wasika ko ba su ba shi ba, an dai maida shi.” Inji Magaji.
Sai dai kuma ya kara da cewa, duk da haka ma’aikatar sa ba ta bai wa Maina wani ofis ko mukami ba, ballantana wani aikin da zai yi.
Maina dai bai halarci zaman kwamitin ba, amma ya tura lauyan sa Sani Kado.
3 – BA MU SAN TA INDA MAINA KE ARCEWA DAGA NAJERIYA BA, inji Kwanturolan Hukumar Shige da fice
Shugaban Hukumar Kula da shige-da-fice, Mohammed Babandede, ya bayyana cewa Abdulrashid Maina baya ga cewa dan Najeriya ne, to a sani cewa kuma dan kasar Amurka ne, domin ya na da fasfo na shaidar kasancewar sa dan kasar Amurka.
Ya ci gaba da cewa cikin Satumba, 2013, EFCC ta tura musu da wasikar kada su bari Maina ya fice daga kasar nan, ko ta ruwa ko ta kasa ko ma ta sama.
Ya so fita a cikin 2013 zuwa kasar waje, amma tun a filin jirgin sama na Abuja, suka hana shi fita.
Cikin 2015, EFCC ta rubuto mana wasikar cewa mu kyale Maina ya tafi duk inda ya ga damar fita, kuma muka yi hakan.
Ya kara da cewa ba su da bayanai na hanya ko hanyoyin da Maina ke bi ya na ficewa daga kasar nan. Domin idan zai fita ko zai dawo, ba ya kai rahoton kan sa kamar yadda dokar kasa ta tanadar a yi ga hukumar shige-da-fice.
4 – MAINA BAI TABA KAI WA EFCC AJIYAR KO KWANDALA DAGA KUDADEN DA TA KWATO BA, inji Magu
Shugaban Rikon Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa Abdulrashid Maina bai taba kai wa EFCC ajiyar ko kwandala daga kudaden da ya rika kwatowa daga barayin kudaden fansho ba.
Ya ci gaba da cewa maganar da Shugaban Hukumar Shige-da-Fice ya yi, cewa EFCC ta bai wa hukumar wasika cewa ta bar Maina ya rika fita daga kasar nan, wato su cire masa takunkumin fita kasashen waje, ya ce EFCC ba ta aika da wasikar ba.
Magu ya ce bai ma san da wannan zancen ba sai a karon farko da aka yi batun a lokacin. Ya kara da nanata cewa shi bai ma san jami’in EFCC din da aka ce shi ya rubuta takardar ba, domin babu sunan sa a hukumar ta su.
5 – JARIDU SUN KARA WA HAYAGAGAR MAINA GISHIRI, inji Lawal Daura
Shugaban Hukumar Tsaro ta sirri, DSS, Lawal Daura, ya bayyana cewa akwai bukatar hukumomin gwamnatin tarayya su rika hada kai da juna sannan kuma su rika tuntubar juna a dukkan al’amurran da suka jibinci ayyukan junan su.
Daura ya kara da cewa rudanin maida Maina aikin sa, duk an kara wa abin gishiri, sannan kuma hayagagar kafafen yada labarai ce ta shige gaba ta rika yi wa batun rakiya har ya kai halin da ake ciki.
Shugaban na ‘yan sandan ciki ya yi wadannan bayanai ne bayan ya tsame kan sa ko hukumar sa daga laifin maida Maina a kan aikin sa da aka yi a asirce.
6 – BA NI NA RUBUTA TAKARDAR MAIDA MAINA BA, inji Abubakar Malami
Shi ma Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayyana cewa bashi ba ne, kuma ba shi da hannu wajen maida Maina kan aikin sa. Malami ya sha ruwan tambayoyi yau a gaban kwamitin binciken yadda aka yi asarkalar maida Maina kan aikin sa a asirce.
7 – RABON DA MAINA YA KARBI ALBASHI TUN 2012, inji Ministar Kudi
Ministar Harkokin Kudade ta ce babu inda ma’aikatarta ta biya albashi ko wasu kudaden alawus ga Abdulrashid Maina tun bayan da aka kore shi, ko aka dakatar da shi daga aiki. Kemi Adeosun ta bayyana cewa rabon da Maina ya karbi albashi tun lokacin da ka dakatar da shi, cikin watan Fabrairu, 2012.
PREMIUM TIMES HAUSA za ta ci gaba da kawo wa masu karatu yadda ta kaya a zaman kwamitin na gaba.
Discussion about this post