PREMIUM TIMES ta lashe kyautar jarida mafi shahara wajen bankado badakalar boye ‘Global Shining Light Awards’ a Kasar Afrika ta Kudu

0

Babban editan jaridar PREMIUM TIMES Moojeed Musikilu da Maya Emmanuel sun lashe kyautar labarin da tafi ko wace labari shahara da labarin da jaridar tayi na tona asirin kisa da birne gawawwakin magoya bayan Kungiyar dake fafutukar kafa Kasar Biafra, IPOB a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Wannan labari ya bankado yadda aka kashe ‘yan IPOB, sannan aka birne su a manya manyan kabururruka ba tare da kowa ya sani ba.

Bayan gano wuraren da aka aikata wannnan abu an dauko hutuna da yin hira da wadanda suka tsira.

Moojeed shine editan wannan labari da Emmanuel Maya ya rubuta a lokacin da ya ke ma’aikaci a gidan jaridar.

Labarin dai itace ta yi fice cikin labaran da aka mika wa masu shirya wannan gasa daga kasashen duniya.

An yi wannan buki na ‘ Global Shining Light Awards’ a kasar Afrika ta kudu.

Share.

game da Author