Osinbajo ya nuna takaicin yadda likitoci ke barin Najeriya

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya nuna takaicin yadda kwararrun likitocin Najeriya ke ficewa daga kasar.

Yayin da yake jawabi a wurin bikin cikar Asbitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan, Osinbajo ya ce a halin yanzu Najeriya na da damar dawo da wadannan dimbin likitoci a gida daga kasashen waje.

Sai ya kara da cewa ba wani abu ba ne ke sa likitoci barin kasar nan su na tafiya kasashhen waje neman aiki sai rashin kyakkyawan tsarin wurin aiki, da kuma matsakar rashin maida hankali wajen kula da fannin lafiya.

Wannan bayani na mataimakin shugaban kasa ya zo kwanaki kadan bayan shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya, NMA, ya bayyana irin matsalolin da ake fuskanta a fannin lafiya a kasar nan.

“A kasar nan kafin maras lafiya ya ga likita sai ya shafe sama da awa biyu. Sama da likitoci 100 sun ajiye aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan a wanan shekara.

‘Kusan likitoci 800 ne suka ajiye aiki a asibitoci daban daban na Legas a cikin shekara biyu, sannan kuma a watan wasu 50 a cikin watan Nuwamba din nan da muke ciki suka ajiye aiki. Inji shi.

“Jihar Kebbi yau shekara biyu kenan ta kasa daukar likita ko guda daya, duk da cewa a kullum sai buga tallar neman likita jihar ke yi a jaridu. Sama da likitoci 200 da nas-nas suka ajiye aiki a Asibitin Ladoke Akintola a cikin wannan shekara.

“Kashi 75 bisa 100 na likitocin Najeriya na shirin ficewa daga kasar nan, har ma su na ta daukar jarabawar tafiya aiki wasu kasashe.” Inji shi.

Share.

game da Author