Osinbajo, Ribadu da dimbin jama’a sun yaba halayen mawallafin PREMIUM TIMES

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya bi sahun dimbin ‘yan Najeriya da suka taya Mawallafi kuma Shugaban Jaridar PREMIUM TIMES, Dapo Olorunyomi murnar cika shekara 60 da haihuwa.

A wani bikin murnar ranar haihuwar mawallafin da aka yi wa shirin bazata, wanda abokan sa suka shirya masa, a Fraser Suites a Abuja, mataimakin shugaban kasa ya ce ‘‘Dapsy mutum ne nagari kuma na kwarai mai zuciya da kishin ganin ya dora duk wanda ke karkashin sa a kan kyakkyawar turba.”

Osinbajo ya ce ya san Olorunyomi kusan tun kamar shekaru 20 da suka gabata, kuma “tun da na san shi har yau ya na daya daga cikin sahihan mutanen da na taba hulda da su.”

“Dapsy mutum ne na kwarai, mai mutunci, dan’uwa kuma aboki, wanda ya zame wa mutane da dama tabaran hangen nesa, ciki kuwa har da ni da yawan wadanda ke wurin nan a yanzu.”

“Ina taya ka murnar cika shekara 60 a duniya. Allah ya kara maka wasu shekarun 60 nan gaba.”

Shi ma tsohon shugaban hukumar Yaki da Cin Hanci, Almundahana da Zambar Kudade, Nuhu Ribadu, ya bayyana Dapo a matsayin haziki kuma gagarabau wajen yaki da cin hanci da rashawa, domin ya yi aiki a hukumar a lokacin da Nuhu din ya ke shugabanci.

Ribadu ya kara da cewa a lokacin da ya ke aiki, Dapo ne babban gogarman yaki da cin hanci da rashawa a EFCC.

Ya ci gaba da cewa, “dawowar da Dapo ya yi nan Najeriya bayan maida mulki ga farar hula, kusan shi ne silar kafuwar sabuwar alkiblar yaki da cin hanci da rashawa.

Mallam-Nuhu-Ribadu-paying-tribute-to-Dapo

“A kasar Amurka na fara haduwa da shi, na ce masa ‘ka dawo Najeriya, ya ce to ya amince.”

“Mutane da dama sun fi sakewa su na bai wa Dapo wasu bayanai dangane da masu wawurar kudin kasar nan, fiye da ni a lokacin da muke aiki tare da shi. Na taba ce masa, kai, ban fa dawo da kai Najeriya ba da nufin ka kwace min mukami.”

“Lokacin da nace wa Obasanjo zanyi aiki da Dapo, sai ya dan sha jinin jikin sa, ya ce min ka san fa su ‘yan jarida za su yi iya kokarin su domin su ga sun bayyana gaskiya, ta yadda za su cimma wata manufa ta su.”

“Ba ma a nan kasar ba, a duniya kaf, za a dade ba a manta da gudummawar da Dapo ya bayar ba.”

Sauran wadanda suka yi jawabin jinjina wa mawallafin na PREMIUM TIMES, sun hada da Shugaban Kamfanin Dillacin Labarai, Bayo Onanuga, wanda a tare suka kafa mujallar THE NEWS cikin 1993 tare da Dapo. Ya bayyana Dapo da cewa kwararren dan jarida ne, kuma dan-takifen da ba ya tsoron fada wa aradu.

Idowu Obas, Ropo Sekoni duk sun yaba wa Dapo tare da nuna shi a matsayin mutum mai zuhudu, wanda abin duniya ko tara abin duniya ba ya gaban sa.

Tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa, Sani Zorro, ya bayyana shi a matsayin shugaban ‘yan jarida masu binciken kwakwaf, wanda ya ce ya san shi tun cikin 1991, kuma ya karu sosai da dimbin ilimi daga wajen Dapo.

Hon-Sani-Zorro-paying-tribute-to-Dapo

Shi ma Babban Editan PREMIUM TIMES, Miskiliu Mojeed, ya ce Dapo mutum ne nagari kuma na kirki wanda ya karu sosai da shi a rayuwar sa.

Ya kuma yi bayanin irin gaganiyar da suka sha wajen kafa jaridar kafin ta samu karbuwar da ta samu a cikin kankanin lokaci, da kuma rayuwar can baya da suka keto a aikin jarida.

Musikilu-Mojeed-E-in-C-Premium-Times-paying-tribute-to-Dapo

Dapo ya kammala Jami’ar Obafemi Owolowo ta Ife, ya yi karatu a waje, kuma ya sha samun kyautuka da dama saboda kwazon da ya ke nunawa wajen aikin jarida.

Da shi aka kafa Mujallar THE NEWS a cikin 1993, sai dai kuma yayin da marigayi Sani Abacha ya taso ‘yan jarida Dapo ya yi gudun hijira zuwa Amurka a cikin 1995.

Ya dawo Najeriya cikin 2004, ya yi aikace-aikace, har zuwa matsayin shugaban Ma’aikatan EFCC a zamanin Nuhu Ribadu.

Da shi aka yi jaridar NEXT, ya yi yakin neman zaben Nuhu Ribadu a 2011, daga nan kuma ya kafa PREMIUM TIMES.

A jihar Legas ma abokan sa sun hada masa irin wannan buki ranar Alhamis.

A wajen bukin Dapo ya koka da yadda cin hanci da rashawa ya ke neman ya lashe aikin jarida a kasar nan.

Ya ce yanzu aikin na neman ya fi aikin dan sanda lalacewa wajen karban cin hanci da rashawa da ta yi kaurin suna da shi.

” Yanzu abin ya kai makura domin daga ciki ne ake aikata abin ba daga waje ba. Irin haka ne ya sa wasu a Majalisar Kasa suke hana wasu ‘yan jarida shiga majalisar don daukar labarai lokacin da shuagabn kasa ya zo gabatar da kasafin kudi. Irin haka duk yana da nasa ba ne da yadda abubuwa suka lalalce a aikin.

Ya yi kira ga ‘yan jarida da su mai da hankali wajen fadin gaskiya maimakon neman abin duniya.

Share.

game da Author