Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bada hayan wani gidan sa mai dakuna 25 haya kan naira 10 duk shekara don samar wa daya daga cikin sabbin yankunan ci gaba da gwamman jihar Ogun Ibikunle Amusun ya kirkiro.
Gwamnan jihar Ogun ya kirkiro yankunan ci gaba guda 52 a jihar domin samar wa mazauna karkara ababen more rayuwa.
Obasanjo ya bada hayan ne a a matsayin nashi gudunmuwar ga wannan abun arziki da gwamnan yayi.
Shugaban yankin ci gaba na Coker-Ibogun, Juwon Gbadebo ya yi tattaki na musamman zuwa majalisar dokokin jihar don sanar musu wannan abin alkhairi da Obasanjo yayi wa mutanen yankin.