Kungiyar Malamai NUT a jihar Kaduna ta sanar cewa za ta shiga yajin aiki daga ranar 23 ga watan Nuwamba.
Kungiyar tasanar da haka ne ranar litini cewa malaman makarntun firamare da na Sakandare a jihar za su shiga ya jin aiki muddun gwamanan jihar bai canza shawarara sa ba da korar malaman da basu ci jarabawar gwaji da aka yi wa malaman jihar ba.
Shugaban kungiyar malaman Audu Amba, y ace sun yi kokarin ganara da gwamnan amma ya ki ji saboda haka yanzu basu da abin da za su iya yi in ba fara yajin aikin ba.
“ Mun amince da gwajin da gwamnan yayi amma mu mun ce a mai da sakamakon gwajin ya zama kashi 60 mai makon 75 da aka sa sannan wadanda basu ci ba a tura su tirenin.
“ Mun rubuta ma gwamna kada ya saki sakamakon jarabawar ya yi mana kunni uwar shegu. Saboda haka babu ruwan mu da matakin da ya dauka.
Bincike da mukayi ya nuna cewa wasu makarantun kusan kowa ne ya fadi jarabawar inda z aka ga mutum uku ne kawai suka rage cikin malamai 50.
Shugaban hukumar SUBEB Nasir Umar ya ce hukumar ta kammala shirin musanya malaman da sabbi domin zuwa yanzu mutane sama da 13,000 sun aiko da takardun neman aikin malunta a jihar.
Discussion about this post