NAZARI NA MUSAMMAN: Tsakanin Maina, Majalisa da Gwamnati: Wane ne mai gaskiya?

0

Nazarin da ke a kasa, bayanai ne na karimtsa da rimatson harkallar da aka shafe shekara da shekaru ana satar hakkin kudaden fanshon tsoffin sojojo da tsoffin ‘yan sanda da wasu masu hakkin da manyan ma’aikatan gwamnatin Nijeriya su ka tauye wa hakkokin su. Sannan kuma bayani ne dauke da yadda aka rika kwato kudaden da kuma yadda a karshe aka zargi masu kwato kudaden da laifin karkatar da wasu zuwa aljifan su.

Mai yiwuwa idan aka yi wa wannan nazari rubutun zube, mai karatu zai dauki lokaci kafin ya fahimta. Don haka, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo muku wannan harkalla daki-daki domin a fi sauri da saukin fahimta:

1. KAFIN SHEKARAR 2011: Kafin 2011 har ma cikin 2011 din kasar nan ta fada cikin rudanin matsalolin da tsoffin sojoji da tsoffin ‘yan sanda suka shiga wajen kin biyan su kudaden fansho na shekara da shekaru, wanda ya rika sanadiyyar daruruwan su tarewa Abuja domin neman hakkin su.

2. HALIN KUNCIN TSOFFIN SOJOJI DA ‘YAN SANDA: Da yawa sun rika mutuwa a wurin jiran kudaden su ko dai a gidajen su ko kuma a bakin ofishin kula da fanshon sojoji ko na ‘yan sanda. Wasu ma sun rika kwana a kangaye, daji da karkashin gada a Abuja duk wurin neman hakkin su.

3. GANO BARAYIN KUDIN FANSHO: Ana cikin wannan ne aka gano cewa tun tuni dai Majalisar Tarayya ta amince a rika biyan tsoffin sojoji, ‘yan sanda da sauran su hakkin su. Kuma kowace shekara ana ware kudin, amma ma’aikatan gwamnati ne ke yin rub-da-ciki da kudin.

4. KAFA KWAMITIN KWATO KUDADEN FANSHO: Cikin watan Janairu, 2011 ne Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a lokacin mulkin Goddluck Jonathan, Stephen Orosanye ya kafa kwamitin da zai kwato kudaden fansho tare da yi wa hukumar fansho din garambawul. Aka rada wa wannan kwamiti suna Pension Reform Task Force Team.

5. SU WA NE ‘YAN KWAMITI?: Wani Mataimakain Darakta a Gwamnatin Tarayya mai suna Abdulrashid Maina, shi ne shugaban wannan kwamiti na tafi –da- gidanka. Akwai wakilan Sufeto Janar na ‘Yan sanda, wakilan Shugaban EFCC, na SSS, Na Shugaban Ma’aikatan Gwamatin Tarayya da na sauran hukumomin tsaro duk a cikin kwamitin.

6. MAJALISAR TARAYYA FA?: A Majalisar Dattawa kuwa akwai kwamiti musamman mai kula da harkar kudaden fansho dama tun tuni, wadda Sanata Aloysious Etuk ne shugabanta, sai Sanata Kabiru Gaya na mataiamakin sa.

7. FARA AIKI DA KAFAR DAMA: Kwamitin Maina bai dade da fara aiki ba, sai ‘yan Nijeriya suka rika kwana su na tashi da labaran yadda kwamitin ke bankado rikakkun barayin kudin fansho daga cikin manyan ma’aikatann Gwamnatin Tarayya.

8. YABO DAGA ‘YAN Nijeriya: Nan da nan sai kwamitin Mania ya rika samun yabo da sam-barka daga jama’a da dama, musamman ganin yadda kwamitin ke fallasa wadanda suka tauye wa tsoffin sojoji da tsofiin ‘yansanda da sauran su hakkin su na shekara da shekaru. Suka ba su cikin kunci su kuma sun azurta kan su da iyalan su.

9. BILIYOYIN DA AKA RIKA GANOWA: Labaran da su ka rika cika jaridu a lokacin masu daukar hankali a kullum su ne yadda kwamitin Maina ya bankado kudaden da suka hada da: (1) A duk shekara barayin fansho na sace naira bilyan 63.6 daga asusun biyan kudin fansho; (2) Wani ofishin ma;aikatan gwamati biyu kacal su na sace naira bilyan 5.32 a duk shekara da sauran ire-iren wadannan labarai marasa dadin ji.

10. DA DAN-GARI AKAN CI GARI: Tun tashin farko kwamitin Maina ya gano cewa ashe wannan daka-daka da harkalla duk da sanin wasu manyan jami’an gwamnati da manyan jami’an tsaro ake yin ta. Ko dai tare suke yin kashe-mu-raba, ko kuma ana ba su na su kason, ladar-ganin-ido.

11. AN FARA SHARI’A SABANIN HANKALI: Yayin da tafiya ta fara nisa ana damke barayin kudin fansho tare da kwace kadarori da rufe asusun ajiyar su na banki, sai aka fara samun sabani da tankiya. Na farko Majalisar Dattawa ta rika zargin Maina da wawurar kudaden da kwamitin sa ke tarawa, musamman ganin cewa shi ma Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Steve Oranye da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa, Aloysious Ekut kan kudaden fansho, da manyan jami’an tsaro duk an same su da hannu dumu-dumu a satar kudaden.

12. RESHE YA JUYE DA MUJIYA: Majalisa ta nemi Oronsanye da Maina su bayyana a gaban ta, domin su yi bayanin bilyoyin kudaden da aka yi zargin sun kwato, sannan kuma suka sace. Orosanye ya je, kuma an maka shi kotu, an ci gaba da shari’a. Shi kuma Maina ya ki zuwa a bisa zargin sa cewa manyan da ake hada baki da su ana cin kudin fansho ne ke son kulla masa sharri ta hanyar neman ganin bayan sa, domin ya rufe musu hanyar wawura.

13. AN BUGA TANDAR NEMAN MAINA: Majalisar ta nemi a kamo Maina a duk inda ya ke. Shi kuma sai ya garzaya kotu, ya nemi a hana kama shi. An yi ta kai ruwa rana ita kuma kotu har karo uku ta na hana a kama Maina.

14. MAINA: DOKIN MAI BAKI YA FI GUDU; Maina ya rika yin hira da jaridu ya na bayyana irin nasarorin da ya samu, tare da fallasa yadda Majalisar Dattawa, manyan jami’an ‘yan sanda, EFCC da sauran wadanda ya rufe wa kofar wawura cewa su ne ke neman ganin bayann sa.

15. ZARGIN KISAN MAINA: Maina ya rika yin ikirarin cewa ana kokarin kashe shi, domin an yi yunkurin haka har sau uku kamar yadda ya yi zargi tare da bayar da hujjojin yadda aka rika kai masa hari a Abuja, ya na mai cewa kuma duk harin da ka kai masa ya na kai rahoto ga rundunar ‘yan sanda.

16. KUDADEN DA MAINA YA CE YA KWATO: A tattaunawar da Maina ya sha yi da jaridu, ya ce kwamitin sa ya bankaro kudade da kadarorin da ya kwato ga manyan jami’an gwamnati sun kai adadin naira tiriliyan 1.63. Ya ce an tsane shi ne kuma ana neman halaka shi domin ya fallasa harkallar da manyan kasar nan ke yi, ciki har da shugaban kwamitin fansho kan sa, Sanata Aloysious Ekut.

17. KABIRU GAYA YA CE MAINA YA SACE NAIRA BILIYAN 195: Tsohon shugaban Kwamitin Inganta Sha’anin Fansho, Abdulrashid Maina, wanda wani kwamitin bincike na Majalisar Dattawa ta zarga da handame naira bilyan 195 a can baya, ya bayyana cewa ya soma fuskantar matsaloli ne tun bayan da ya ki amincewa da ya bai wa ‘yan majalisar cin-hanci. Cikin 2012 Sanata Kabiru Gaya ya zarge shi da badakalar kudi har Naira Bilyan 195.

18: TUBKA DA WARWARAR SANATA KABIRU GAYA: Sai dai kuma cikin shekara ta 2016, ranar 3 Ga Afrilu, 2016 Sanata Kabiru Gaya ya yi wata tattaunawa da jaridar THE SUN TA TURANCI inda ya yi bayanin da ke nuna cewa sun samu kudin a wasu ma’aikatu da kuma hukumomi a ajiye. Idan haka ne, ina matsayin Maina a yau?

SANATA KABIRU GAYA A JARIDAR SUN: “Idan Za ku iya tunawa, na yi sanata a zangon majalisa na 6 da na 7 kafin yanzu na 8 da muke a ciki. A zango na 7 mun binciki badakalar kudin fansho. Mu biyu ne shugabannin kwamitin. A lokacin, mun yi nasarar gano wasu makudan kudade har Naira Bilyan 195 da ke kimshe a cikin asusun ajiyar wasu ma’aikatu daban-daban da kuma wasu hukumomi. Kuma kudaden duk na fansho ne kuma ba a yi amfani da su ba.”

Haka Sanata Kabiru Gaya ya bayyana a cikin hirar ta sa da THE SUN, a shafi na 15.

19. MAINA YA TSERE: Za a iya cewa tun ma kafin ya tsere, Maina ya dade ya na wasan buya, domin ya ki yarda a kama shi, a bisa dalilin cewa za a iya halaka shi, kuma babu abin da za a yi, wanda ya mutu sa ta kare kenan. Daga baya kuma ya tsere ya bar kasar.

20. YA GUDU, BAI HAKURA BA: Tun bayan da Kabiru Gaya ya yi bayanin cewa wadannan kudade naira bilyan 195, su na cikin Asusun Bai Daya na Gwamnatin Tarayya, sai Maina ya shiga kamfen amma ya na a boye cewa to ga gaskiya fa ta bayyana, su Kabiru Gaya da suka ce ya sace naira bilyan 195 a 2012, yau ga hi a cikin 2016 ya fadi muhimmancin tsarin TSA a karkashin mulkin Buhari, har ya buga misali da wasu kudi na fansho naira bilyan 195 da ya ce su na ciki ajiye. Ya yi ta yi wa su Kabiru Gaya Allah ya isa da kuma kokarin neman hakki a kotu. Dama kuma Maina ya sha fitowa ya na yin tir da bankaurar shari’a ko hukuncin da kotu ta yanke wa wasu gaggan barayin kudaden fansho da ya kamo.

Idan ba a manta ba, kwamitin Maina ya kama wasu manyan ma’aikatan gwamnati shida, aka kwace manyan tulin gidajen da suka mallaka daga satar kudaden fansho, sannan kuma aka gurfanar da su kotu a bisa zargin wawurar naira bilyan 32.8 na kudin fansho. A cikin su akwai Esai Dangabar, Shu’aibu Taidi da John Yakubu, wadanda alkali ya ci su tarar da kowanen su a ta kai ta naira milyan daya ba. Wannan hukunci ne ya tayar da kura sosai a kasar nan.

21. MAINA YA NEMI DAWOWA YA TAIMAKI GWAMNATIN BUHARI: A tsawon lokacin da Maina ya yi a boye, a kullum maganar sa ita ce babu wanda ya fi shi sanin yadda ake satar kudin kasar nan. Ya na mai ikirarin cewa shi ba barawo ba ne. Domin bas hi kadai yay i aikin kwato kudade da kadariri ba, akwai jami’an tsaro kuma kowane Sgugaban Hukumar Tsaron bangaren sa ne ya turo shi, sannan kuma sun a kai musu rahoton duk abin da ke faruwa. Idan aka bas hi dama, to zai yi wa Gwamnatin Buhari aiki fiye da EFCC da ICPC, domin su wadannan hukumomi, ba su bincike har sai an kai musu kara, korafi, gulma ko kuma an hura wa wani usur.

22. WASU HUJJOJI DA AKE ZARGIN MAINA: Duk da cewa a kullum ikirarin Maina shi ne shi ba barawo ba ne, PREMIUM TIMES can baya ta buga wasu hujjoji na wasu kudaden da aka gano a wasu asusun ajiyar banki cewa nasa ne. Kazalika kuma kwanan nan an gano wasu gidaje masu tsadar gaske da aka ce mallakain sa ne.

23. RINCIMIN DAWO DA MAINA A ASIRCE: PREMIUM TIMES ce ta fallasa labarin yadda aka dawo da Maina ya ci gaba da aikin sa a matsayin sa na ma’aikacin gwamnati a asirce. Wannan labari ya zubar da kimar gwamnatin Buhari, su kuma tsakanin wadanda ake zargi kowa ya yi ta kaucewa daga laifin shi ne ke da alhakin dawo da Maina har aka maida shi aikin gwamanti. Hakan ya zubar da mutun cin gwamnatin Buhari, kuma an rika yin shakkun yadda wasu makusantan shugaban kasar ke daukar gaban-gabarar zartas da wasu hukunce-hukunce ba tare da sanin shi shugaban kasa ba.

24. TAMBAYOYIN DA BABU AMSA: Me ya sa Maina ba zai je kotu ba, idan ya na da gaskiya? Me ya sa wasu hukumomin tsaro ke kare Maina su na ba shi kariya? Me ya sa aka sake barin Maina ya boye ko ya sulale? Me ya sa Fadar Shugaban Kasa ta wofintar da batun dawo da Maina?
Me ya sa aka dawo da Maina? Shin an dawo da shi ne domin ya taimaki gwamnati wajen yaki da cin hanci da rashawa? Me ya sa wadanda suka dawo da shi ba su bada shawarar ya kai kan sa kotu ko Majalisa ba, domin ya fara wanke kan sa kafin a maida shi akan aikin sa? Su wa ke neman halaka Maina, kamar yadda ya yi ikirarin ana neman halaka shi?

25. INDA MAGANA TA KWANA: A yanzu da Majalisar Tarayya ta nemi wadanda ake zargi da bayyana domin jin yadda aka sarkala Maina cikin gwamnati a asirce an kuma bankado yadda aka yi watandar gidaje da fankama-fankaman rukunonin gidaje har 222 wadanda kwamitin Maina ne ya kwato su, amma wasu suka rabas da su a tsakanin su. Ganin irin yadda aka fara shari’a sabanin hankali ne ya sa PREMIUM TIMES HAUSA ke tambaya: Shin tsakanin Maina, Majalisar Dattawa da Gwamanti, wa ke da gaskiya?

Share.

game da Author