Najeriya ta tanadi abincin kauce wa yunwa a 2018 – Minista

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta tanadi isasshen abinci da zai wadaci kasar nan, domin gudun afkawa matsalar karancin abinci a shekara mai zuwa ta 2018.

Ministan Gona Audu Ogbe ne ya bayyana haka a Katsina ranar Lahadi da ta gabata.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron hadin-guiwa tsakanin Hukumar IFAD da Gwamnatin Tarayya kan batun canjin yanayi da kuma dabarun inganta harkokin noma.

Babban Mashawarciya kan dabarun noma na ma’aikatar mai suna Auta Appeh ce ta wakilci minista a wurin taron, a Katsina.

“Wasu jihohi a Arewa maso Gabas da sauran yankunan kasar nan ka iya afkawa cikin matsalar karancin abinci a 2018 a dalilin canjin yanayi.

“To amma maganar za a fuskanci yunwa ma ba ta taso ba, domin ina tabbatar muku da cewa mun tanadi wadataccen abincin da zai magance duk abin da ka iya tasowa.”

Sai dai kuma ministan ya shawarci manoma da su daina sare itatuwa barkatai, domin bishiyoyin su na da amfani wajen raya wurare. Ya ce sare itace ya na rage wa kasa karfi da kwari da kuma nagartar amfanin gonar da za a shuka a cikin ta. Sannan kuma ya na janyo zaizayar kasa da dumamar canjin yanayi, wadanda ke yi wa al’umma illa sosai.

Ta bayyana cewa a duk shekara Hamada na yi wa Najeriya barazana inda ta ke shigo mu kusan kilomita 12 a kowace shekara.

Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya, NAN, ya kawo rahoton cewa Kungiyar Abinci da Harkokin Noma ta yi kintacen cewa amfanin gona a wasu jihohi a shekara mai zuwa ba zai kai karshen damina ba, sakamakon lattin fara ruwan shuka da za a fuskanta a 2018.

Share.

game da Author