Uwargidan marigayi Abdulmumini Dame dan majalisar dokokin jihar Taraba, Rukkayya ta maka ‘yan uwan marigayin a kotu kan muzgunamata da fatattakar ta da suka yi daga gidan mijin ta bayan rasuwar sa.
Marigayi Abdulmumini dake wakiltan Ardo-Kola ya rasu a watan Oktoba a asibitin FMC Yola bayan rashin lafiya da ya yi fama da shi.
Rukkayya ta ce kiyayyar da ke tsakanin ta da ‘yan uwan mijin ta ya kara zafi ne bayan rasuwar sa.
” Ko da na aure shi ba mu haihuba wanda hakan ya sa ‘yan uwan sa ke yi mini gori duk lokacin da muka hadu.”
Ta ce rikicin ya fara ne tun lokacin da ‘yan uwan mijin ta suka hana ta shirya birne mijin ta kamar yadda shari’ar musulun ci ya gindaya wai su basu san shi a matsayin musulmi ba.
” Sun ce wai dan uwansu ba musulmi bane saboda hakan bai kamata a birne shi a matsayin musulmi ba.”
Kanin sa mai suna Denis ya ce a sanin sa da dan uwan sa addinin kirista ya ke bi har ya rasu saboda haka babu abinda zai sa su bari a birne shi a matsayin musulmi.
Sai dai uwargidan marigayi Abdulmumini ta musanta abinda Denis ya ce cewa ya na da masaniyar cewa mijin ta ya musulunta shekar 9 da suka wuce kafin ma ya aure ta daga gidan su.
” Dalilin hakan ne na ruga babbar kotu dake Jalingo ranar 30 ga watan Oktoba na shigar da kara sannan kotun ta bada umurnin cewa a dakatar da duk wani shirye shiryen birne miji na.”
” Duk da wannan umurni da kotun ta bada Dennis tare da ‘yan uwan sa suka sace gawan sa daga dakin ajiye gawa dake asibiti suka birne shi yadda suke so amma a bangare na mun yi masa sallah duk da rashin gawar.”
sai da Dennis ya ce babu aure tsakanin dan uwansa marigayi Abdulmumini da Rukkayya ko a can da ma, zaman zina suke yi kawai sannan dan uwansa bai musulunta ba kamar yadda ta ke ta cewa. Sanna ya shigar da kara a wata kotun daban.
Discussion about this post