Sakataren hukumar kula da ilimi na jihar Neja Yahaya Garba ya ce hukumar ta dakatar da wani mataimakin shugaban makaranta Mohammed Mohammed da aka kama ya dirka ma wata ‘yar aji uku (JSS3) mai suna Faith Danjuma ciki.
Ya ce bayan hukumar ta sami labarin aika aikan da ya yi ne suka kafa kwamitoci guda biyu domin yin bincike kan gaskiyar lamarin.
Ya ce kwamitocin za su aika da sakamakon binciken da suka yi ma’aikatar ilimin jihar.
Garba ya ce sun gano cewa Mohammed ya yi wa ‘yar aji uku Faith Danjuma ciki ne bayan gwajin cikin da aka yi mata a asibiti.
Bayan haka kuma hukumar gudanarwan makarantar ta ce zata hukunta malamin kamar yadda doka ta ce sannan zai ci gaba da kula da yarinyar sannan za a canza masa makaranta zuwa na maza kawai.
Daga yanzu kuma rabin albashi za a dunga biyan shi har na dan wani lokaci kafin a kammala komai.