Wata mata ta maka mijin ta a kotu a Abuja, tana rokon ta da ta raba auren su saboda gazawa da mijin ta yake yi wajen wadatar da ita a wajen jima’i.
Matan mai suna Kate Ude, yar shekara 32 ne.
” Miji na ba namiji bane. Na yi hakuri amma ya kai ni makura. Duk lokacin da muka zo kwanciya sai kaga ya kasa yin komai sai kame-kame. Sannan cikin minti daya sai kaga wai har ya gama.”
Ta roki kotu da ta war-ware wannan aure ko ta nemi wanda ya yi daidai da ita.
Da yake fadin na sa bayanai a kotu, mijin ta mai suna Micheal ya ce sau dayawa takan bukace shine lokacin da shi kuma baya bukatan ta shine yasa sai abin ya gagara kuma shi baya shan wani magani domin samun karfin saduwa da matar sa.
Shima ya ce araba auren.
Alkalin Kotun, ya daga ci gaba da sauraronkaran sai watan Fabrairun 2018.