Jiya ne akaba bada labarin rasuwar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Elex Ekweme, wanda shi ne mataimaki ga Alhaji Shehu Shagari, wanda yay i shugabanci tsakanin 1977 zuwa 1983.
ASHAFA MURNAI Ya tsakuro wani yanki na tarihin rayuwar sa a lokacin da ya na yaro. Wannan zai kara tabbatar wa mai karatu wata karin magana da Hausawa ke cewa: “Idan ka ji wane ba banza ba, idan ba a sha dare ba an sha rana.”
PREMIUM TIMES HAUSA ta tsakuro wannan bayanan ne daga wata hira da aka yi da shi, wadda PREMIUM TIMES ta buga cikin Nuwamba, 2013.
1. Shi ne dan Nijeriya na farko da ya fara kafa kamfanin zane-zanen taswirar gidaje da gine-gine a Najeriya.
2. Ya na karatun digirin-digirgir aka ce ya dawo Nijeriya ya zo ya shiga siyasa. Ya dawo, ya zama mataimakin Shehu Shagari.
3. Ya auri matar sa tun ta na kwaila ‘yar shekara 12.
4. Mahaifin sa Kirastan Misau ne wanda ya rika yawo kauyuka ya na maida kabilun Igbo Maguzawa zuwa addinin Kirista.
5. A kauyen Uga aka haife shi, a cikin harabar wani Cocin Mishau da ke kauyen, wanda mahaifin sa shi ne limamin cocin.
6. A kasa ya rika zuwa firamare daga Uga zuwa Oko, tafiyar kilomita 8 zuwa da dawowa.
7. Kullum da asubahi ake tashin sa su tafi makaranta. Sai sun je korama sannan za su yi wanka. Daga can sai su dau hanyar tafiya makaranta.
8. Mahaifin sa ya rasu a 1942. Mahaifiyar sa ta haifi ‘yan-biyu bayan mutuwar mahaifin nasa. Tsananin rayuwa ta sa mahaifiyar sa ta kasa ciyar da shi, sai wata Antin sa ta dauke shi riko.
9. Tazara zuwa makaranta ta karu saboda ya koma wani kauye mai nisa a hannun Antin sa.
10. Duk lokacin da ya yi latti, ya na shan dukan tsiya a makaranta.
11. A cikin hirar da Premium times ta buga a 2013, Ekweme ya ce, “Shi aka yi wa juyin mulkin 1983, ba Shagari ba.
Saboda su Buhari ba su so idan Shagari ya gama wa’adin sa, Inyamiri ya zama shuagabn kasa. Dalili kenan inji shi aka kifar da Shagari tun da wuri, kafin a fara shirye-shiyen kamfen idan wa’adin zango na biyu na Shagari ya kusa karewa.
12. Ya ji haushin Buhari sosai, saboda ya daure shi a 1983. Ekweme ya ce bai kamata a tsare shi a kurkukun Kirikiri ba, shi kuma Shagari wanda shi ne shugaban kasa kuma shi ake zargi da lalata Najeriya, a yi masa daurin-talala a cikin wani gida.
Discussion about this post