Wani jigo a jam’iyyar PDP Abdullahi Jalo, ya ce shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya, Ahmed Makarfi ya sanar masa gaba da gaba cewa zai fito takarar shugabancin kasar nan a inuwar jam’iyyar PDP bayan an gudanar da gangamin jam’iyyar na kasa a watan Disamba.
Wasu ‘yan jam’iyyar na kokawa da Makarfi cewa yana nuna ma wadansu ‘yan takara musamman masu neman shugaban cin jam’iyyar fifiko akan wasu. Domin har wasu na kira da ya sauka daga kujeran shugaban cin jam’iyyar kafin zaben jam’iyyar na kasa.
A haka kuma da yawa ‘ya’yan jam’iyyar sun gargadi uwar jam’iyyar cewa muddun suka kasa yin abin da ya dace a zaben to fa zasu fice daga jam’iyyar su kafa wata sabuwa.
Daily Trust da ta ruwaito wannan labari, ta kara da cewa Makarfi ya karyata wannan korafi sannan ya ce Abdullahi Jalo ba kakakin sa bane. Abin da ya fadi, ra’ayin sa ne amma ba daga bakin sa ya fito ba.