Majalisar Tarayya ta kammala shirin daukaka karar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke kan Sanata Ali Ndume, inda ta ce dakatarwar da aka yi masa haramtacciya ce.
Babbar Kotun ta kuma umarci Majalisar Tarayya ta biya shi dukkan hakkokin sa na albashi da alawus-alawus na tsawon watannin da aka dakatar da shi.
Lauyan Majalisar, Mike Ozekhome ne ya fitar da sanarwar daukaka hukuncin zuwa kotu ta gaba a yau Litinin.
Idan ba a manta ba, a ranar 30 Ga Maris ne majalisar ta dakatar da Sanata Ndume, wanda shi ne tsohon Shugaban Masu Rinjaye, har tsawon watanni shida.
An dakatar da Ndume ne a bisa dalilin ya nemi majalisa da ta binciki wani korafi da jama’a ke yi dangane da Shugaban Majalisa, Bukola Saraki da Sanata Dino Melaye.
Maimakon haka, sai aka dakatar da Ndume har tsawon shekara daya.
Sai dai kuma an dakatar da shi tsawon watanni shida kawai, “saboda kokarin da ya yi na tozarta Sanata Melaye da majalisar gaba daya.”
Kan haka ne Ndume ya je kotu, inda a karshe aka ba shi gaskiya, tare umartar majalisa ta biya shi albashin sa na wata shida da dukkan sauran alawus-alawus da ya cancanci karba a wadannan watanni shida.