Majalisar Dattawa ta tattauna kan kirkiro sabbin Cibiyoyin Kiwon Lafiya a kasar nan

0

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta amince da kiraye kirayen da a ke yi na kafa asibiti mallakar gwamnatin tarayya a kowani yanki na kasar nan.

Majalisar ta ce yin haka zai sa wadanda ke ganin ba a yi musu adalci ba rashin kafa irin wadannan asibiti a yankin su su dai na fadin haka.

Sanata Mathew Urhoghide dake wakiltar Edo ya jagoranci tattaunawar a zauren majalisar.

Sanata Urhoghide ya ce ya kawo wannan zance zauren majalisa ne ganin yadda ake ta cece-kuce kan hakan musamman yankunan da basu da shi.

” Dalilin haka ne ya sa mazauna garuruwan da basu dashi ke yin dogon zango domin samar ma kansu ko ya’yan su magani a wasu asibitocin.”

Daga karshe, majalisar ta yanke shawaran cewa kwamitin ta na kiwon lafiya ta gudanar da bincike kan haka sannan ta mika mata biyanai kan abin da ta samo domin daukar mataki na gaba.

Share.

game da Author