Ma’aikatar Makamashi da Wutan lantarki ta barnata sama da dala miliyan 300 – Inji Dino Melaye

0

Sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye ya sanar wa majalisar dattawa cewa ma’aikatan makamashi da wutan lantarki karkashin jagorancin Babatunde Fashola ta barnata kudaden har dala miliyan 385 na kwangilolin ayyukan wutan lantarki a kasa Najeriya.

Dino ya ce wannan kudade babu sa hannun majalisar kasa aka dibe su don yin wadannan ayyuka.” Har yanzu da nake sanar daku wannan ayyuka har yanzu babu wanda akayi ko kuma a ba da rahoton ana yi kuma duk an ba ‘yan kwangila kudaden da suke bukata don ayyukan.”

” An ba IBEX dala miliyan 300 cikin kudin sannan kuma an ba kamfanin ‘General Electric’ dala miliyan 30.”

Ya kara da cewa wadannan kudi an fitar dasu ne tun shekarar 2013 kuma har yanzu kashe su akeyi babu wani abu da za a nuna na wai an dan sami biyan bukata.

Share.

game da Author