KWARA: Zamu yi amfani da ma’aikata 3000 a zaben Kananan hukumomi – Hukumar Zabe

0

Shugaban hukumar zabe na jihar Kwara Abdulrahman Ajidaba ya ce sun kammala shiri tsaf domin yin zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar ranar 18 ga watan Nuwamba.

Ajidaba ya ce mutane 11,000 suka cika fom din neman aiki da hukumar ranar zabe duk da cewa mutane 3000 ne hukumar ke bukata.

Ya ce an yi jarabawa domin daukar wadanda ake bukata cikin duk wadanda suka nemi aikin. Ya ce kwananan za su fito da sunayen wadanda aka dauka domin horas da su kafin zaben.

Share.

game da Author